AFCON 2023: Tsohon ɗan majalisar Nijeriya ya mutu a wajen kallon wasan Super Eagles da Afirka ta Kudu

Daga BASHIR ISAH

Bayanai da MANHAJA ta samu na nuni da cewa wani tsohon dan majalisar wakilai daga Jihar Delta ya mutu a wajen kallon wasan kwallon da aka buga tsakanin Super Eagles da Afrika ta Kudu na gasar AFCON 2023 a ranar Laraba.

Wata majiya ta kusa da ahalin marigayin ta ce, Ojuogboh ya yanke jiki ya fadi ne a lokacin da aka bai wa Afirka ta Kudu damar buga fenariti a kurarren lokaci a yayin wasan da aka buga a filin Stade de la Paix da ke Bouake.

A halin rayuwarwa, marigayi Cairo Ojuogboh tsohon dan Majalisar Wakilai ne daga jam’iyyar APC wanda ya wakilci Mazabar Ika a Jihar Delta.

Haka nan, ya taba rike mukamin Babban Daraktan Hukumar Bunkasa Yankin Niger Delta (NDDC).