Mace ’yar jarida ta fi namiji samar da gamsasshen rahoto kan cin zarafi – Salamatu Abdullahi

“Mata ne suka fi dacewa da aikin jarida”

Daga AISHA ASAS

Bakuwar tamu ta wannan makon dai bata buqatar doguwar gabatarwa, saboda kasancewarta ‘yar gida ga kaso mafi yawa daga cikin masu karatunmu, musamman ma mazauna Jihar Kaduna. Duk da cewa, fuskarta da gangarar jikinta bata kewaye Arewacin Nijeriya ba, sai dai tuni amon sautin muryarta ya karade mutanen Arewa, musamman ma ma’abota sauraron littafan Hausa.

Kwararriya ce da ta qware wurin iya sarrafa murya yayin karanta littafan Hausa, kuma tana gabatar da shiri na musamman domin kawo gyara ga zamantakewar aure. ’Yar jarida ce da ta yi aiki a gidajen radiyo da dama, kuma ta ke bayar da gudunmawa wurin wayar da kan al’umma ta bangarori da yawa.

A tattaunawar Manhaja da ita, za su san ababen da ba ku sani ba game da ita, tun daga tarihi, gwagwarmaya da kuma wasu batutuwa da suka shafi aikin jarida da kuma rayuwarta a ciki. Idan kun shirya, Wakiliyar Blueprint Manhaja, AISHA ASAS, ce tare da Salamatu Bello Abdullahi:

MANHAJA: Sunanki sananne ne, don haka tarihin rayuwarki ne bukatar masu karatunmu.

SALAMATU: Salamatu Bello Abdullahi, haifaffiyar garin Lere ce, Karamar Hukumar Lere ta Jihar Kaduna. Na yi karatun firamare a LEA Lere, sannan na yi makarantar gwamnati da ke Lere a matakin sakandare, wato Government Secondary Lera. 

A shekarar da zan gama, Allah bai sa na gama ba, na yi aure. To, cikin ikon Allah shi mijin da na aura, bayan har na haihu daya har biyu ma, sai ya ga dacewar in koma makaranta. To a haka dai na gurgura, da aurena da ‘ya’yana, kai tsaye na koma ajin karshe a babbar makaranta. Akai jarrabawar duk da ake yi na kammala karatu da ni.

Bayan sakamako ya fito, na nemi gurbin karatu a Nuhu Bamali Polytechnic da ta ke Zaria. A nan na karanci aikin jarida, wato ‘Math Communication’. A takaice, tahirihin Salamatu kenan.

Wasu na ganin aikin jarida ba na mata ba ne, musamman ma matan Arewa. Menene na ki ra’ayin?

A gani na, idan ana maganar aikin jarida, mata ne ya fi dacewa su yi aikin jarida, ko in ce suna layin wadanda ya kamata ace akwai su a aikin jarida. Me ya sa na fadi haka, saboda akwai wuraren da dama mata ne kawai za su iya samo ainihin sahihin abinda yake faruwa a wani lamari.

Bari in ma ki misali, yanzu a ce an samu wata matsala a cikin gida, mace za ta iya shiga gidan gaba-gadi don dauko rahoton abinda ya faru, wanda a lokuta da dama yake yi wa maza wahala. Duk da ita kanta mace a wasu lokuta sai ta nemi izini kafin shiga kamar yadda namiji ya zame masa dole, sai dai ko kadan ba irin neman izinin namiji zata yi ba, wanda hakan zai bata damar samo rahoton sama da shi.

A wani vangare idan muka koma kan sha’ani irin na cin zarafin mata da ake yi, mace ‘yar jarida ta fi namiji damar samo irin wanna rahoto yadda ake bukata, domin an ce wai, ‘ciwon ‘ya mace, na ‘ya mace ne’. Ko a wurin tambayar ma mace ta fi namiji sanin irin tambayoyin da ya kamata ta yi a irin wanna matsala. Don haka ni a tunanina, aikin jarida na da matukar muhimmanci ga ‘ya mace. Ko a shirin da nake gabatarwa a yanzu na ‘Firarmu Ta Mata’, kinga ni mace ce, na san irin lalurori da zafi da radadin da muke ji a gidanmu na aure, don haka duk macen da ta zo min da matsalar na san ta yadda zan iya kwantar mata da ranta, in bata hakuri ta sanadin ni mace ce.

A matsayinki ta mace ‘yar jarida, wane irin kalubale ki ka fuskant a aikin?

Ai Anty Aisha, a cikin kowane aiki akwai nasara akwai rashin nasara, akwai kalubale. Ta bangare na zan iya cewa, kalubalen da ya faru da ni, ko in ce na ci karo da shi a aikin jarida bai ma can dade ba. Akwai wani shiri da nake gabatarwa na mata kamar yaddana fada a baya, mai suna ‘Firarmu Ta Mata’, kuma kowa ya san idan aka ce firarmu ta mata, ya san ababe ne da suka shafi rayuwar mata, matsalolin da suke fuskata a gidanjen mazajensu har ma da abinda ya shafi nasarorin da suke samu a rayuwar ta aure.

Duk da hakan, bai hana mu waiwaye kan mazan da nasu masalolin ba, duba da cewa, muna wani zamani da za mu iya cewa kusan ake kunnen doki wurin tarayya a matsalolin aure tsakanin matan da mazan. Don haka muna bada dama ga mata da idan suna da matsala su kawo mana ita, mu kuwa za mu bude matsalar sosai, mu tattauna kanta, kafin daga bisani mu mika wa masu sauraro, inda a nan za a bata shawarwarin da lokuta da dama ake samun mafita kan damuwar.

To su ma mazan sukan samu irin wanna damar, su ma mu tattauna matsalar kamar dai yadda muke yi wa ta mata. Kuma shi wannan shiri ka’idar shi ba a fadar sunan mai matsala ko wata alamar da wani zai iya gane shi.

Da wannan ne zan zo kan amsar tambayar da aka yi min, kalubalen da na fuskata shine, a wata rana, wani bawan Allah, ya yi tattaki har wurin aikin namu, ya kawo min ziyara. A lokacin zan tuna ba ni da ma aiki a ranar, na dai shigo ne, sai aka ce min Ina da bako a ‘reception’.

Na je muka gaisa, ya nuna yabawa da jinjina kan shirin da muke gabatarwa, ya ce, yana jin dadin shirin. Daga karshe ya sanar da ni yana tafe da tasa matsala ce.

Daga nan ya fara karanto min; shekaran shi 14 da matarshi, ‘ya’yansu hudu, da sauransu. matsaloli dai da yake fuskata, ga shi kuma auren na gida ne, ‘ya’yan maza suke shi da matar, kuma irin auren nan ne na zaman gidan gado, ga dakin mata, ga na uwar miji, babban gida dai a takaice. Ya dai fere min biri har wutsiya.

To cikin ikon Allah, da na kawo wannan matsala tasa a wannan shiri, kwalliya ta biya kudin sabulunta, domin an ciza, an hura kwarai da gaske, inda dukka vangarorin biyu muka tatava, kowa da irin mafitar da zai bayar tsakanin ni da abokan aikina guda biyu da muke gabatar da shirin tare da kuma masu sauraron mu. Daga karshe ya dauki shawarar da yaga ta fi mai, ya aiwatar.

To ranar kafin ya tafi, na ce masa mu yi musanyar lambar waya, don zan so idan ka je wurin ita matar taka zan so ka kirani sai mu yi magana da ita, don jin inda ta dosa da kuma jin matsalar ta bangaren ta.

A takaice dai daga karshe muka yi nasarar kone wannan matsalar har ma matar tasa ta dawo dakinshi. Domin har iyayen sun yi iya kokarin shirya abin, sun kasa, amma cikin yardar Allah, Ya ba mu damar yin hakan.

A ranar da ta koma gidansa, ya daga waya ya kira ni, bayan mun gama gaisawa, ya sanar da ni dawowar ta matar tasa, har ya ba ni ita muka gaisa, na dan kara yi mata nasiha cikin wasa, na ai ta hakuri da sauran su. Daga wannan magana muka yi sallama, ban kara magana da su ba, sai wata rana da ya kira mu gaisa, har nake ce masa ai wata rana zan zo musamman don in ga uwar gida.

Ranar Ina zaune, sai naga wani sako ya shigo a wayata, ya turo min, cewa wai wuri kaza(anan Jihar Kaduna ya ambata) suna da matsalar ko tsaro ne ya ce, na dai manta zubin sakon yake. To da yake ni tsarina, bana bada damar cigaba da hulda da mutum bayan bukata ta biyu, matsalar ce ta hada, tunda ta biya mun gama, sai kuma idan ka sake samun wata matsala gaba. To da wannan ne ya sa ban bi ta kan wannan sakon ba, don sanin dalilin sa.

Sannan Ina da dabi’ar idan sakwani suka yi min yawa, na kan duba wadanda ba su da muhimmanci in dinga goge su, don haka wannan sakon na daya daga cikin irin sakwanin da na goge a lokacin.

Daga wannan sakon dai bai kara turo wani ba, kuma bai kara kira na ba, ni ma ban neme shi ba, sai dai number shi na nan ajiye a akwatin lambobi na wayata. Tsayin lokaci, kafin wata rana, na tashi, Ina shirin zuwa wurin aiki, sai ga kira da wata bakuwar lamba, “don Allah Ina magana da Salamatu ne?” Na ce masa eh, sunana Salamatu. “Don Allah muna neman ki ne a nan State CID,” inji shi. Na ce, Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Wallahi Anty Aisha ba zan iya misalta ma ki irin tashin hankalin da na shiga ba. Sai zufa nake yi duk da safiya ce lokacin. Na ce, CID? To a nan ne yake tambayata ko na san shi wannan bawan Allah da nake magana kansa.

Daga baya dai ya tambaye ni a ina nake aiki. Na sanar da shi. Ya ce “kin shigo wurin aiki ne?” Na ce a’a. Ya ce, idan na shigo in sanar da shi.

Jikina na rawa na isa wurin aiki, ko karyawa ban yi ba. Bayan na sanar da shi zuwana, suka iso. Dama na sanar da ‘producer’ na da sauran wadanda muke aiki tare, na nemi su jira mu ji da me za su zo, don haka da suka zo na tafi tare da shi, har shi wanda muke magana da shi ya ce ya zan zo masu da wasu.

Na ce, ai dole tunda dai wanda yake magana kansa ya shafe mu dukka, saboda dai da su nake abinda ya zama silar haduwa ta da shi.

To fa daga nan ne ya fito da wayarshi, ya nuna min hoton wannan mutumin a duqe, an daddaure hannayenshi, daga gani kasan ya daku. Ya ce na gane shi. Na amsa. Ya tambaye ni tsayin shekara nawa, na ce ba a ma cika shekara daya ba.

Suka nemi bayyani na mu su dalla-dalla. A nan suka nuna min wanna sakon da ya turo min a takarda tare da numbar wayata, wanda shine dalilin da ya sa suka neme ni.

Lamarin dai da aka yi ta maida magana tsayin lokaci kafin na samu kaina. Wallahi sai da na dauki sati ba na cikin hayyaci na, kowa ya kale ni, ya san Ina cikin tashin hankali.

Shin wannan lamari da ya faru bai sare ma ki gwiwa ba, har ki ka ga barin aikin jarida a matsayin mafita?

Da wanna tambayar za mu dasa aya, wadda muke fatan bakuwar tamu ta bude mana da amsar ta kafin sauran tambayoyin.