Daga BASHIR ISAH
Shugaban Kasa Bola Tinubu ya janye niyyarsa ta zuwa kallon wasan karshe da Nijeriya za ta kara da Côte d’Ivoire a gasar AFCON 2023 da ke gudana a kasar Côte d’Ivoire.
Maimakon haka, Tinubu ya wakilta Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima kan ya jagoranci tawagar Shugaban Kasa zuwa wajen kallon wasan wanda za a buga a ranar Lahadi.
Hadimin Shugaban Kasa kan sha’anin yada labarai da sadarwa, Stanley Nkwocha, shi ne ya bayyana haka a ranar Asabar.
MANHAJA ta rawaito da fari cewar, Tinubu zai halarci kallon wasan na karshe da Nijeriya za ta buga da Côte d’Ivoire domin karfafa wa ‘yan wasan gwiwa.
A cewar Nkwocha, “Gwamnatin Tarayya ta bukaci ’yan Nijeriya, wadanda ke gida da na ketare, da su hade kai wajen mara wa Super Eagles baya.”
Idan za a yi iya tuna, ko a wasan na kusa da na karshe da Nijeriya ta kece reni da Afirka ta Kudu, Shettima ya wakilci Tinubu wajen kallon wasan don karfafa wa ‘yan wasan gwiwa.
