Daga BASHIR ISAH
Shugaban Bankin Access kuma Shugaban Kamfanin Acess Holdings, Hebert Wigwe, ya mutu a hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu da ya rutsa da shi a Amurka.
Matarsa da ɗansa da wasu pasinjoji uku na daga cikin waɗanda hatsarin ya rutsa da su wanda baki ɗaya sun riga mu gidan gaskiya.
Hatsarin ya faru ne a birnin California na ƙasar Amurka.
MANHAJA ta kalato cewa, marigayan sun shiga jirgin ne da nufin zuwa kallon wasan ƙwallon ƙafar da Super Bowl za ta buga a Las Vegas.
Jaridar New York Times ta tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ba ta bayyana ko su wane ne ragowar pasinjoji ukun da suka rasa ransu a hatsarin ba.
