Daga BASHIR ISAH
Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana mutuwar Babban Shugaban Kamfanin Access Holdings plc, Herbert Wigwe, a matsayin babban rashi ga masana’antar banki a Nijeriya.
Cikin sanarwar manema labarai da ya fitar ta hannun kakakinsa, Sulaiman Bala Idris ranar Lahadi a Gusau, babban birnin jihar, Lawal ya nuna alhininsa game da rasuwar Herbert Wigwe.
Marigayin ya ra su ne a wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu da ya rutsa da shi da matarsa da kuma ɗansa a California ta ƙasar Amurka.
A cewar Lawal, “Da rasuwar ‘ Wigwe, na yi rashin aboki wanda ya bada gudummawa matuƙa ga ɓangaren harkokin bankin a Nijeriya.
“Margayi Herbert Wigwe ya bar alama muhimmiya a masana’antar banki a Nijeriya ta hanyar aiki tuƙuru da sadaukarwa.
Shugaban Bankin Access da iyalinsa sun mutu a hatsarin jirgin sama a Amurka
Gwamnatin Zamfara ta fara biyan tsoffin ma’aikatanta bashin giraduti na N13.4bn
“Mun yi mu’amala da marigayi Wigwe a harkokin banki a lokutan baya.
“Da fatan Allah Ya bai wa ahali da makusantan Wigwe haƙuri da juriyar wannan rashi. Haƙiƙa, ba za mance da shi ba,” in Lawal.
