Shugabancin MOPPAN: Yadda Barde ya zama magajin Sarari a Kannywood

Daga AISHA ASAS 

A ranar Laraba da ta gabata, 31 ga Janairu, 2024, Kwamitin Amintattu na Kungiyar Masu Shirya Finafinai ta Kasa, wato MOPPAN, ya nada Mallam Habibu Muhammd Barde, Mataimakin Shugaba na Shiyar Arewa ta Tsakiya na kungiyar, a matsayin shugaban riko na kasa.

Sanarwar nadin na kunshe ne a cikin sanarwar manema labarai da Kwamitin Amintattu na kungiyar ya fitar mai dauke da sa hannun shugaban kwamitin, Makama Sani Mu’azu, wanda ya biyo bayan ajiye mukamin da Dakta Ahmad Sarari ya yi a matsayin Shugaban Kungiyar, duka dai a ranar ta Larabar.

Sarari ya bayyana cewa, ya ajiye mukamin ne a bisa ra’ayinsa, amma ba don wani abu ba. Ya bayyana hakan ne a cikin sanarwar manema labarai da ya fitar a ranar Laraba.
Kamar yadda Manhaja ta ruwaito, a cikin sanarwar, ya yi bayanai da dama ciki har da irin nasarorin da MOPPAN ta samu a karkashin jagorancinsa.

“Da suanan Allah mai rahama mai jinkai. Tsira da aminci su tabbata ga Manzon tsira Annabi Muhammadu S.A.W.

“Ina mai godiya ga Allah S.W.T da ya nuna mana wannan rana kuma ya ba mu ikon yin abinda ya samu na shugabancin kungiyar MOPPAN.

“Duk abin da yake da farko yana da karshe, Allah ne kadai ba shi da farko ba shi da karshe. Kamar yau ne ‘ya’yan wannan masana’anta suka nemi na fito takarar zama shugaban kungiyar MOPPAN na kasa, na amsa kira aka yi zabe, kuma aka sami nasara, sannan wa’adin farko ya kare aka sake neman na sake tsayawa duk da na yi furucin cewa ba ni da sha’awar cigaba. Cikin ikon Allah zangon farko na shekara biyu da zango na biyu na shekara biyu sunzo karshe.

“Duk da dai taron koli (Congress) na kungiyar MOPPAN da aka yi a ranar 10 ga watan Yuni 2023 ya amince da karin shekara guda ga shugabanni na kasa da na jihohi bisa tsarin da ke cikin sabon kudin tsarin mulki na MOPPAN (MOPPAN Constitution 2022). Sauka ta daga mukamina bai yi karo da kudirin taron kolin ba (National Congress), hakan yana da alaka ne da ra’ayina da akida ta.

“Sauran zababbu za su ci gaba da shugabanci a karkashin jagorancin daya daga cikin mataimakana wanda yake kula da bangaren Arewa ta Tsakiya, wato Malam Habibu Muhammad Barde, har izuwa 31/1/2025.

“Mun dauki alkawarin yin duk wani aiki bisa doron kundin mulkin MOPPAN kuma mun yi alkawarin riqe amanar wannan kungiya da masana’anta.

“Mun gudanar da ayyukanmu bisa doron kundin tsarin mulkin kungiya. Sai dai dan kuskure na ajizanci da ba a rasa ba.

“Ina mai miqa godiya ta ga dukkannin shugabannin MOPPAN da suka gabaceni da Amintattun MOPPAN da Abokan aikina da aka zabe mu tare da shugabannin jihohi. Godiya ta musamman ga masu sukar mu domin su ne suka dinga farkar da mu in mun fara bacci,” inji Sarari. 

“Ya kuma kara da cewa, “Hakika mun sami nasarori masu dimbin yawa kuma mun gamu da kalubale kala-kala sannan kuma mun gaza a wasu wuraren.

“Zan bar MOPPAN mai cikakkiyar rijista, mai amintattun dattawa da gwamnati ta sani, mai ofis da kayan ofis, mai “account” da isassun kuɗi a ciki. Zan bar kungiyar da ba bashi ko na kwabo a kanta, kungiya mai rijista da kyakkyawar alaka da dukkannin hukumomin kasa da na jihohi.

“Ina fatan shugaban riko zai dora a kan abin alkhairin da muka samar kuma zai gyara kurakuren da muka yi, sannan ya ci gaba da da ayyukan alkhairin da muka fara kuma ya gudanar da zabe bisa adalci. Da fatan ‘ya’yan wannan masana’anta zasu zakulo shugabanni na gari da za su iya tunkarar sabon kalubalen da masana’antar take ciki.”

Dakta Sarari ya cigaba a inda ya tunatar da kungiyar irin alkawuran da suka yi gabanin a zabe su a zaben shekarar 2019 inda yake cewa, ‘Kafin ayi zaben MOPPAN a 2019, mun gabatar da kudirorinmu na irin aikin da zamu yi wato “Manifesto”. Munyi alakawarin:

Dawo da darajar MOPPAN musamman a idon gwamnati da hukumomi na kasa da jihohi.

Dawo da rijistar MOPPAN ta hukumar kula da kamfanoni ta kasa wato “CAC” da dawo da sunan kungiyar kan manhajar hukumar.

Gyara kundin tsarin mulkin kungiya.

Ba wa kungiyoyin kwararru (professional guilds and Associations) damar taka rawa a zaben MOPPAN na kasa.

Farfaɗo da harkar kasuwancin fim a masana’antar Kannywood.

Horar da ‘ya’yan kungiya wajen kara musu ilimi da daburun yin fim.

Sanar da ‘ya’yan masana’anta duk irin halin da kungiya ko masna’anta
take ciki.

Hakika mun sami cikakkiyar nasara akan kudirai na 1, 2, 3, 4, da na 5. An gudanar da kudirori na 6 da na 7 amma ba yadda aka so ba.

Akwai cikakkun bayanai na ayyukan da muka yi sama da 100 da irin nasarori da kalubale da gazawar da aka samu a lokacin wannan shugabanci, sannan akwai shawarwari.

A shirye nake na ba wa sabon shuwagabani gudunmawa da ba su dukkannin bayanan da suke bukata.”

Daga karshe, Dakta sarari ya nemi gafara kuma ya sanar da yafewa duk wanda ya yi masa ba daidai ba.

“A karshe ina mai neman gafarar duk wanda na batawa ko ina sane ko bana sane, ni ma na yafewa duk wanda ya bata min ko yana sane ko baya sane.

Allah ya taimake mu ya taimaki Kannywood ya sada mu da dukkannin alkhairan da ke cikin wannan masana’anta ya kuma kare mu daga dukkannin sharrin da ke cikinta.”

Tuni dai Kwamitin Amintattu na kungiyar ya nuna godiyarsa ga Dakta Ahmad Sarari bisa dawainiyar da ya yi da kungiyar wajen ciyar da ita gaba a tsakanin shekarun da ya shafe rike da ita, tare da cire son kai a dukkan lamarin jagorancinsa.

MOPPAN na daya daga cikin fitattun kungiyoyi masu shirya finafinai a Nijeriya, mai mamabobi da dama da kuma rassa a fadin kasa.

Wane ne sabon shugaban riko na MOPPAN?

Malam Habibu Muhammad Barde, ya fito daga Azare ta Jihar Bauchi. Kwararre ne a bangaren ilimin aikin kirkira, kuma tsohon dan jarida da ya yi aiki a gidan talabijin da rediyo da dama a fadin Nijeriya. 

Daga cikin karatukan da ya yi, ya mallaki shedar kammala difloma da kuma digiri a fannin kirkira bangaren aikin talabijin da rediyo, a Kwalejin Columbia, Hollywood CA, Amurka, a shekarar 1983 zuwa 1985.

Sannan ya yi aiki gidan rediyon Bauchi da kuma gidan talabijin na NTA reshen Jihar Bauchi, inda yake jagorantar bangaren wasan kwaikwayo, kafin daga bisani ya koma Birnin Tarayya.

Ya fara da aiki karkashin FRCN,  kafin ya koma aiki karkashin gwamnatin tarayya, tun daga fadar shugaban kasa, zuwa wasu ma’aikatu da dama, kamar Ma’aikatar Tsaro, Ma’aikatar Noma, Ma’aikatar Al’adu da sauransu. 

Kafin ritayar sa daga aiki, Malam Habibu Barde, ya rika mukamai da dama, kamar mataimakin darakta na Inland waterways.

Bayan ajiye aiki, Malam Habibu ya tsunduma aikin finafinai da kuma tsara talla da kuma shirye-shirye ga gidajen rediyo da talabijin ciki kuwa har da BBC.

Sannan ya mallaki digiri din sa na biyu a bangaren na kirkira a Jami’ar Alhmadu Bello da ke Zariya.