’Yan bindiga sun sace darakta kusa da sansanin sojoji a Abuja

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A yayin da ake cigaba da fama da matsalar rashin tsaro a Abuja, a baya-bayan nan dai wannan harin da aka kai wani gida mai tazarar mita 200 kusa da sansanin sojoji da ke Pambara, a karamar hukumar Bwari a Babban Birnin Tarayya Abuja, ya fi daure kai.

A yayin harin, an yi garkuwa da wani mai suna Aondo Ver, wanda aka ce darakta ne a Hukumar Kula da Gidaje ta Tarayya.

’Yan bindigan sun kai farmaki gidan ne da misalin karfe 12:30 na tsakar darebn wayewar garin jiya Alhamis. Rahotanni sun nuna cewa, masu garkuwa da mutanen sun samu haurawa ta katangar gidan ne.

Har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, rundunar sojin ba ta ce uffan ba kan lamarin.

Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan wasu ‘yan bindiga sun shiga wani gida a unguwar Guita, Chikakore, Kubwa, dake yankin Qaramar Hukumar Bwari ta Babban Birnin Tarayya, Abuja, suka yi garkuwa da wasu ‘yan mata ‘yan gida daya.

Masu aikata mugunta suna kai hari ga yara, matasa da iyalai, suna haifar da firgici a tsakanin al’umma.

Su na bayyana cikin tsari mai kyau, su na aiki da rana tsaka, galibi a tsaka-tsaki masu cunkoso ko kusa da wuraren taruwar jama’a kamar kasuwanni da makarantu.

Suna kuma gudanar da ayyukansu cikin dare.
Makonni da suka gabata, masu garkuwa da mutane sun jefar da gawarwakin wasu mutane hudu da suka kashe a kusa da wani tsohon shingen binciken sojoji da ke bayan Junction Idah a kan titin Bwari zuwa Jere SCC a karamar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna.

Daga cikin gawarwakin da aka gano kawo yanzu akwai wata dalibar Sakandare da aka bayyana cewa diyar babban jami’in shari’a na Hukumar Jami’ar Aasa (NUC) haifaffen Jihar Ekiti, Folorunsho Ariyo, da dalibar jami’ar Ahmadu Bello (ABU) Zariya mai mataki aji na 500, Nabeeha Al-Kadriyar.

Yayin da aka yi garkuwa da Ariyo tare da mahaifiyarta da ’yan’uwanta uku a ranar Lahadi biyu da suka gabata, an kama Nabeeha tare da mahaifinta da kuma ‘yan uwanta mata biyar a ranar 9 ga watan Janairu.

A wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan ta fitar a ranar Lahadin da ta gabata, ta sanar da kama Bello Mohammed mai shekaru 28, wanda ake zargi da kisan Nebeeha, a wani samame da a ka yi a wani otel a Kaduna a ranar 20 ga watan Janairu.