Batun matsalar damfara a yanar gizo

Babu makawa ga duk mai mu’amala da yanar gizo (Internet) ko wayar salula ya san matakan kariya game yadda wadansu vata gari ke baza tarko ta ko wacce irin dama su ka samu don su damfari jama’a. Idan muka ce yanar gizo to anan mu na nufin Ko wanne fanni na yanar gizo. Shin kai ma’abocin burauzin ne don karanta labarai, ko mai binciken ilmi, ko ma’abocin kafofin sada zumunci da dai sauran su.

Yau za mu kawo hanyoyin da su ka fi shahara wajen yin damfara a yanar gizo, kuma sanin su zai taimaka ma wajen tsallake tarkon su, kuma har kai ma ka sanar da wadansu.

Hakika a wannan zamani da mu ke ciki a iya cewa yanar gizo ta zama larura a harkokin rayuwarmu na yau da kullum.

A yau yanar gizo ta haifar da saukin gudanar da al’amura cikin. Misali ta yanar gizo za a iya samun labarai da muhimman bayanai na kusan dukkan abin da ya shige maka duhu. Ga kafofin sada zumunta da ke bada damar kulla zumunci tsakanin yan uwa da abokan arziki, ta yadda za ku iya sanin lafiyar juna a kowanne lokaci ku ka so hakan kuma duk nisan da ke tsakanin ku. Sannan ta wadannan kafofi akan sadu da wadanda aka debe tsammanin haduwa don kuwa ta yiwu an rabu ne tun lokacin da ba waya, kuma ba kafofin na sada zumunta.

Hakanan akwai hanyoyin bunkasa kasuwanci, ga hanyoyin aiken kudi duk fadin duniya cikin sauki, biyan kudade, irin na makaranta, wuta, ruwa, tikitin jirgi da dai sauran al’amura masu kama da wannan. Kari akan haka akwai neman aiki, cike takardun makaranta, gudanar da jarabawa, kai abun da yawa wai mutuwa ta je kasuwa inji Bahaushe.

Sai dai abin takaicin shi ne, duk da wadannan alfanu da yanar gizo ke da su ga al’umma, wasu ’yan damfara, maha’inta, masu son cin bulus, azzalumai sun fake da wadannan ni’imomi suna damfarar wadanda ba su ji ba, ba su gani ba, makuden kudade.

Mafi yawan mutane kan fada hannun waɗannan ’yan damfara a rashin sani, wasu kuwa saboda son banzarsu, don kuwa Bahaushe ya ce idan ka ce za ka bani riga to sai na duba ta wuyanka. Kwarai kuwa haka ne, misali, ya za ka ce za ka nuna min hanyar da zan samu Dala 1000 kimanin Naira 300,000 a wuni sannan ladan kudin da za ka nema a waje na bai taka kara ya karya ba? Idan gaskiya ne kai ka bi waccan hanyar mana ka samu wancan kudin mai yawan. Ko ka fi so na da kanka ne?

Don haka mu ka ga zai yi kyau mu nusar tare da nunawa mai karatu musamman wadanda ke fadawa tarkon waɗannan azzalumai a rashin sani, mafi yawa daga ire-iren hanyoyin da su ke bi wajen damfarar mutane. Ba don komai ba sai don sanin hanyoyin da su ke bi zai taimaka ma ka kwarai da gaske ka tsallake duk irin tarkon da za su dana ma ka.

Sannan daga bisani za mu kawo hanyoyin kubuta daga mugun nufinsu, amma da farko zai yi kyau mu jero hanyoyin da su ke bi don damfarar jama’a.

Ga wasu daga cikin hanyoyin da su ke bi nan:

  1. Tallar hanyar samun arziki da gaggawa.
  2. Bukatar ka biya su kudi.
  3. A bukaci ka saukar da (download) wata Manhaja (Software).
  4. Samun kudi ko ribar da ta wuce hankali.
  5. Bayanai masu tsoratarwa.
  6. Neman aiki.
  7. Bayanai masu rikitarwa.
  8. Naci.

Hanyoyin kubuta;

Tunda Blueprint Manhaja ta jerowa mai karatu hanyoyin da su kafi shahara wajen damfara a yanar gizo, yanzu za mu kawo hanyoyin kuvuta a takaice.

  1. Game da sakon imel da su ke aikowa, mafita ita ce matukar ba kai ka bukaci wannan sako ba to ka rabu da shi.

Abu na farko, kar ka kuskura ka latsa inda suka bukaci ka latsa.

Na biyu, ka dakatar da samun sakon. A can kasan ko wanne imel akwai inda ake bada damar tsayar da samun saqo matukar ba a bukatarsa.

Na uku, ka goge sakon, don kar ka manta watarana ka fada tarkonsu.

  1. Game da tura kudi. Ka kiyayi tura kudi akan wani al’amari na yanar gizo ta hanyar ‘transfer’.

Guji tura lambobin katin amsar kudinka (ATM CARD).

Guji tura lambobin sirrinka na banki.

Guji tura lambar shaidar bankinka ta BVN

Idan wani al’amari ya shige ma duhu, tuntuvi sashen kula da abokan ciniki na bankinka don warware ma ka zare da abawa.

  1. Game da arzikin gaggawa.

Ka yi watsi da irin wannan talla karma ka waiwaice shi, sannan ka guji sake ziyartar shafin don kuwa ’yan damfara ne.

  1. Game da samun kudi a kankanin lokaci. Shi ma kamar na sama ne.
  2. Game da neman ka aika musu da kudi. Shi ma kamar na 3 ne.
  3. Game da naci kuwa sai mu ce ka yi uwar watsi da su, sannan ka latsa inda aka ce ‘Spam’ a akwatinka na imel bayan ka bude sakon.
  4. Game da neman aiki. Ka nemi gamsasshen bayani dangane da shafin kafin ka je ga aikewa da takardunka.
  5. Game da samun kudi ko ribar da ta wuce hankali, kamar na uku na sama.
  6. Game da saukar da manhaja. Ka kiyayi saukar da manhaja daga duk ‘website’ da ba ka amince da shi ba.

A karshe, muna kira ga masu karatu a duk lokacin da ka ci karo da wasu shirye-shirye a yanar gizo da kake shakku a kansu, yana da kyau ka tambayi wani da ka ke ganin ya fi ka ido a harkar yanar gizo. Idan hakan ba ta samu ba, to ka lura da sunan da suka bai wa shirin sai ka yi bincike akansa a yanar gizon. Abun nufi anan idan har ka gane sunan shirin sai ka rubuta shi a ‘Google’ don gano gaskiyar al’amarin.

Shi yadda tsarin yanar gizo ya ke, kamar yadda ake samun mutanen banza to kuma haka mutanen kirki na da yawa don haka za su baka bayani dalla-dalla game da wannan shirin ko ‘website’ din. Wani ma za ka tarar an damfare shi ne a wannan Site din sai ya yi rubutu don ya fadakar da wadansu.

Blueprint Manhaja na kira ga hukumomin Nijeriya da su gaggata kawo karshen irin wannan damfare-damfare, ko dai ya yanar gizo ko kuma ta sauran hanyoyi da ke faruwa a cikin kasar.