AFCON 2023: Osimhen na fuskantar matsin lamba wajen zura ƙwallaye – Udeze

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Tsohon dan wasan Nijeriya Ifeanyi Udeze ya ce dan wasan Super Eagles Victor Osimhen yana fuskantar matsin lamba wajen zira kwallaye a gasar AFCON 2023.

An yi hasashen Osimhen ya shiga gasar ta bana a matsayin daya daga cikin ’yan wasan da za su fafata domin samun kyautar dan wasan da ya fi yawan zura kwallaye.

Sai dai Osimhen ya samu nasarar zura awallo daya ne kawai kuma ya rasa damar cin kwallo da dama.

Da yake waiwayar rawar da Osimhen ya taka bayan wasanni uku na rukuni, Udeze ya yi imanin cewa rashin samun karin kwallaye yana shafar kwarin gwiwarsa.

“A gare ni Osimhen yana cikin matsin lamba, shi ya sa yake kokarin duk mai yiwuwa don zura kwallo,” inji Udeze a gidan rediyon Brila FM.

“Matsi yana shafar shi kuma ina tsammanin matakin amincewarsa ya ragu kadan a duk lokacin da ya fuskanci matsayin abokin hamayya, don haka yana bukatar ya dawo da kwarin gwiwa.”

Tauraron dan wasan na FIFA 2002 ya ce har yanzu yana da kwarin gwiwa kan dan wasan.

Ya kara da cewa, “Osimhen dan wasa ne mai kyau kuma na yi imani da shi kuma ina yi masa fatan alheri.”

Osimhen dai zai yi fatan samun takalminsa na zura kwallo a raga yayin da zakarun na AFCON sau uku suka shiga zagaye na 16.

Eagles dai sun kammala gasar a matakin rukuni da maki bakwai bayan wasanni uku, inda suka zura kwallaye uku aka zura musu kwallo daya.