EFCC ta fara bincike kan badaƙalar jirgin ‘Nigeria Air’ daga Sirika – Keyamo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta fara gudanar da bincike a kan wata badakalar cinikin jirgin ‘Nigeria Air’ da tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika ya kulla.

“Hukumar EFCC na binciken wannan yarjejeniya,” Ministan Sufurin Jiragen Sama da Cigaban Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya bayyana a cikin shirin Siyasa A Yau na Channels Television a ranar Laraba wanda Blueprint Manhaja ke sa ido.

Ya ce “akwai binciken manyan laifuka. Na kira ga rahoton”.

Keyamo ya kuma ce babu wani kamfanin jirgin sama na cikin gida da za a nada a matsayin jirgin sama na kasa, ya kara da cewa “za mu kafa jirgin da ya dace na kasa”.

A watan Agustan da ya gabata, jim kaɗan bayan an rantsar da shi a matsayin minista, Keyamo, Babban Lauyan Nijeriya (SAN), ya sava wa yarjejeniyar da Sirika ya yi, ya kuma dakatar da duk wani tsari da aka yi gaggawar bayyana shi kwanaki har zuwa karshen gwamnatin tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, don ba da damar tantance kwangiloli yadda ya kamata.

Takaddamar da ta biyo bayan kafa kamfanin jigilar jiragen sama na ‘Nigeria Air’, ya tilastawa tsohon ma’aikacin jirgin saman, murabus daga mukaminsa na shugaban kamfanin jiragen saman kasar Habasha.

Shugaban rikon kwarya na Nigeria Air na wancan lokacin, Kaftin Dapo Olumide, ya ce jirgin da aka yi amfani da shi wajen kaddamar da fara ayyuka a kasar, hayarsa aka yo daga kamfanin Ethiopian Airlines, ya kara da cewa an mayar da jirgin zuwa kamfanin Ethiopian Airlines bayan an kaddamar da shi a ranar karshe ta gwamnatin Buhari a watan Mayu.

Majalisar Dattawan Nijeriya da kwamitocin majalisar wakilai kan harkokin sufurin jiragen sama duk sun bayyana kaddamar da jirgin Nigeria Air a matsayin yaudara.

Babu gudu ba ja da baya kan mayar da FAAN zuwa Legas.

Keyamo ya kara da cewa babu gudu babu ja da baya kan batun mayar da hedikwatar hukumar kula da filayen jiragen sama ta kasa (FAAN) daga Abuja zuwa Legas.

“Muna ci gaba. An ba da umarnin,” in ji Ministan.

Sanata Ali Ndume daga Borno ta Kudu da kuma jiga-jigan kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF), Northern Elders Forum (NEF) da sauran kungiyoyin Arewa sun yi fatali da matakin da FAAN da Babban Bankin Nijeriya (CBN) suka yi, inda suka yi ta raɗe-raɗin cewa yunkurin mayar da Arewa saniyar ware.

Sai dai Keyamo ya dauke hedkwatar hukumar ta filin tashi da saukar jiragen sama ya zama tilas ne daidai da yanayin tattalin arziki da aiki na yanzu.

Keyamo, ya ce mayar da hedikwatar hukumar ta FAAN za ta ceto gwamnati da al’ummar Nijeriya rabin Naira biliyan da jami’an hukumar suka yi asarar tikitin jirgin da za su tashi daga Legas zuwa Abuja su dawo.

Ministan ya ce manyan jami’an hukumar ta FAAN da kungiyoyin jiragen sama sun tuntuve shi cewa a mayar da babban ofishin hukumar zuwa Legas domin gudanar da ayyukansu.

Akan ko Shugaba Bola Tinubu ya san hukuncin ko bai sani ba, ya ce, “Na dauki matakin; hukunci ne a karkashin kulawar minista”.