Tsaftace zuciya a game da batun kishi (1)

Tare da AMINA YUSUF ALI

Assalamu alaikum. Masu karatu sannunku da jimirin karanta wannan fili namu na Zamantakewa wanda yake zuwar muku kowanne mako a jaridarku mai farin jini ta Blueprint Manhaja. A wannan makon za mu tattauna a kan zafin kishin mata da ya addabi al’umma da abin da yake kawo shi, da kuma yadda za a magance shi. A sha karatu lafiya.
Kafin na shiga rubutun gadan-gadan.

Ya kamata na tuna wa ‘yanuwana mata cewa: mu ne jinsin da muka fi nuna muna da hadin kai yayin da wata ‘yaruwarmu ta shiga wani hali fiye da maza. Kuma mu ne kullum muke iqirarin cewa ciwon ‘ya mace na ‘ya mace ne. Wato duk abinda ya samu mace daya, to ya shafi dukkan mata. Amma abinda zai ba da mamaki. Daga maganar namiji ta gifta tsakaninki da ‘yaruwarki, sai kuma zancen ya sauya.

Ya zama kuma macen ce take jefa ‘yaruwarta a lalurar. Maimakon ta zama mai magance mata. Wato dai mai dokar bacci ya vige da gyangyadi. Duk da dai wasu lokutan a kan samu matan da suke rike ‘yanuwansu cikin amana.

Misalin irin wannan shi ne; yadda kishiya take zaluntar kishiyarta saboda sun hada miji. Kuma kowacce ba ta da burin a ce dayar aurenta ya mutu ta fice ta bar mata gidan. Ko mu dubi yadda uwar miji kan gallaza wa surukarta ko yadda suruka take gallaza wa uwar miji. Ko kuma yadda dangin miji mata suke gallaza wa matar danuwansu.

Idan kuma damar a hannunta take ta gallaza musu. Ko kuma mu dubi yadda matar Uba kan zalunci ‘ya’yan miji da makamantansu. Abun dai ba sauki ko ta wanne ɓangare. Amma abin tambayar me ya sa sai mu mata, mata, mata! Ba don kada ma a ce na matsa da yawa ba, sai na ce; ko qannen miji maza da suke gallaza wa matar wansu. Yawanci idan ka bincika za ka ga akwai zugar mace a ciki.

Amma abin mamakin sai ka ga mun fi kowa ihu da tutiyar mace ta mace ce. Bayan kuma idan muka nutsu za mu ga dukkan ciwon da ya addabi mace, wata macen ce sila. Ko neman mata da maza suke yi suke cutar da matansu da wa suke yi? Da wata macen suke yi ‘yaruwarta. To ina mafita? Anya kuwa ciwon ‘ya macen na ‘ya macen ne?

‘Yaruwa ki sani, kafin ki zama kishiya, ko dangin miji ko matar Uba, da sauransu. Sai da kika fara zama musulma. To kamata ya yi ki fara sa hakkin ‘yanuwartakar musulunci fiye da komai a mu’amalarku. Ba a ce dai ki zauna a cuce ki, ko a tauye miki hakkinki ba. Amma ki nemi hakkinki ba tare da kin cutar da kowa ba.

Da farko dai zan fara da Uwargida. Ba don komai ba don ita ce ta fari kuma Hausawa sun ce daga na gaba ake ganin zurfin ruwa. Kuma kishi ya fi zafi daga uwargida. Domin kusan dukkan labaran idan ma ba dukkansu ba. Da suke ta yawo na zafin kishi yawanci iyayen gida su suka fi wuce gona da iri. Iyayen gida su ne kan gaba wajen daukar ran kishiyoyinsu ko na mazajensu yayin da suka yi yunkurin yi musu kishiya.

Wannan yana faruwa ba don komai ba sai don rashin son wata macen ta shigo gidanta ta yi tarayya da ita a kan mijinta da kuma dukiyarsa, kada a dada kada a rage. To kun ga wannan ya sava da koyarwar musulunci da kuma halin nagarta. Kishi na musulunci wanda matan Annabi S.A.W suka yi, shi ne na yin rigegeniya wajen kyautata wa miji. Ba wai kokarin sai an cutar da kishiya ko an fitar da ita ba. ‘yanuwa ku sani, baqin kishin nan zai iya jawo miki asarar Lahirarki. Kishiya ba daga kanki aka fara ba, dagawar ta mecece?

Ya ke Uwargida ki sani: kasancewarki ta farko a wajensa ba wayonki ba ne ko dabararki ba ce, ko zabinki ba. Allah ne ya kadarta cewa ke za ki fara zama matarsa. Kuma ki sani a kan jarrabawa kike. Allah jarraba ki yake don ya ga gudun ruwanki. Kuma ki sani, wannan matsayin naki na Uwargida idan kika yi zalunci zai iya kai ki ga halaka ta Duniya da Lahira. Haka ki sani, shi auren da mijinki ya ƙaro ba wai cin amanarki ya yi ba.

Hakkinsa ne da Allah Ya ba shi na ya karo mace daga daya zuwa hudu, idan har zai yi adalci. Saboda haka dagawa da ji da kai ba naki ba ne. Da ke da wacce aka auro duk hakkinku daya a wajen mijinku. Haka Allah ya shar’anta. Al’ada ce kawai ta mayar da ke Uwargida. Idan kika yi wasa da hakkin Allah kuma kika sa girman kai kika bijirewa Allah, Shi ma zai iya nuna miki mulkinsa a kanki kuma ya zare albarka da walwala a rayuwarki.

Shi kansa mijin da kike takama, A zare albarkar dake dukiyarsa. Don haka ki daure zuciyarki ki yi komai cikin tsoron Allah. Ke ma ba ki san naki yaran ina za su je ba. Ki sani ita ma Amaryar ba son ranta ne ta aure miki miji ba. Ita ma da so samu ne, za ta samu kamar taki, da ta fi son ta auri mijinta ta zauna daga ita sai shi. Amma ita ma wata jarrabawa ce a kanta da aka kadarta ta auri naki mijin.

Za mu ci gaba a wani makon insha’Allah.