Ƙasurgumin ɗan fashin dajin da ya addabi Birnin Gwari ya shiga hannu a hanyarsa ta zuwa kafa sansani a Kano

Daga BASHIR ISAH

Jami’an tsaro a Kano sun cika hannu da gawurtaccen dan fashin dajin nan da ya addabi yankin Birnin Gwari, Isah Lawal.

Dan bindigar ya fada a komar ‘yan sandan ne bayan da ya shirya zuwa kafa sansani a Kano inda aka same shi dauke da shanu 55 da tumaki guda shida, kamar yadda Kakakin ‘Yan sandan Kano, ASP Abdullahi Haruna ya bayyana a ranar Litinin.

‘Yan sanda sun ce wanda ake zargin a baya mazaunin kauyen Kaya ne da ke yankin Karamar Hukumar Giwa a Jihar Kaduna.

Jami’an sun ce dan fashin dajin ya yi ikirarin cewa suna kokarin tserewa ne daga sansaninsu na Maidaro a Birnin Gwari biyo bayan rasa wani njigonsu mai suna Bashir da suka yi a Malumfashin Jihar Katsina a wani artabun da suka yi da wasu kishiyoyinsu.

 Ya kara da cewa, wannan ne ya sa suka baro inda suke da nufin zuwa kafa sabon sansani a dajin Gwarzo-Karaye da ke Kano.

‘Yan sanda sun ce suna kan zurfafa bincike kasancewar wanda ke hannu yana taimaka musu da muhimman bayanan da za su taimaka musu wajen dakile ‘yan fashin daji a jihohi makwabtan Kano.

Kawo yanzu dai Kwamishinan ‘Yan Sanda na Kano, Mohammed Usaini Gumel, ya ba da umarnin a tura karin dakaru da kayan aiki zuwa kan iyakokin Jihar Kano.

Daga nan ya yi kira ga al’ummar jihar da su rika taimaka wa ‘yan sanda da muhimman bayani. Kana ya bada lambaobin da za a iya tuntubarsu kamar haka:  08032419754, 08123821575, 09029292926 da dai sauransu.