EFCC ta tsare ƙanin Hadi Sirika kan binciken badaƙalar N8bn

Daga BASHIR ISAH

Jami’an Hukumar Yaki da Rashawa (EFCC) ta tsare Abubakar Ahmad Sirika, kani ga tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Abubakar Sirika.

News Point Nigeria ta rawaito cewar, jami’an sun cika hannu da dan’uwan tsohon ministan ne a ranar Lahadi bayan da binciken da EFCC ke gudanarwa a Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama ya biyo ta kansa.

Ana zargin Sirika da tafka almundahanar da ta kai N8,069,176,864 a lokacin da yake rike da mukamin Minista.

Hukumar ta ce kudaden na wasu kwangila ne guda hudu wanda Sirika ya bai wa wani kamfani mai suna Engirios Nigeria Limited mallakar kanin nasa.

Majiyar News Point Nigeria ta ce, Sirika ya bai wa kaninsa Abubakar kwangila duk da sanin cewa shi din ma’aikacin gwamnati ne kuma mataimakin darakta a Ma’aikatar Albarkatun Ruwa ta Tarayya, inda ya fara aiki tun a shekarar 2000 zuwa yau.

Kwangilolin da ake batun sun hada gina wani bangar na Filin Jirgin Sama na Katsina kan kudi N1,345,586,500, gina cibiyar kula da motar kashe gobara a Filin Jirgin Saman Katsina kan kudi biliyan N3.8.

Aikin sayo na’urorin sanyaya wurin da gina dakin janareta da sauransu a Aviation House da ke Abuja kan kudi miliyan N615, sai kuma aikin sayo wa Kwalejin Fasahar Tukin Jirgin Sama ta Nijeriya da ke Zariya kayan aiki kan kudi biliyan N2.2.

Majiyar ta kara da cewa, a halin da ake ciki Abubakar Sirika na hannun EFCC inda yake ci gaba da bada karin bayanai game da binciken da take kan gudanarwa a Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama musamman a wa’adin da Hadi Sirika ya yi yana rike da ma’aikatar.