Yadda manyan Arewa suka kassara cigaban yankin da al’ummarsa 

Daga NAFI’U SALISU

Idan aka yi maganar tushen tattalin arziki da tarin dukiya a Nijeriya yankin Arewa ne, haka nan idan ana maganar ƙasar noma da yin kiwo duka yankin Arewa ne aka san nan ce tushen duk wani arzikin Nijeriya. Sanannen abu ne cewa ita kanta ƙasar an gina ta ne da arzikin da yankin Arewa ke samarwa har ƙasar ta kawo zuwa wannan lokaci da arziki ya havaka bila-adadin, ta yadda masu hannu-da-shuni suka bunƙasa, suka yi ɗaukaka ta fannin kasuwanci da tara dukiya mai yawa a yankin Arewacin Nijeriya.

Na daɗe ina nazari tare da lura da yadda Nijeriya ke tattare da arzikin ƙasa (musamman yankinmu na Arewa), da kuma yadda kowanne yanki a ɗaya ɓangaren na Nijeriya ake ƙoƙari da hoɓɓasar ganin an samar da abubuwan ci gaba na zamani tare da daƙile duk wani abu da zai iya zamowa ƙalubale ga jama’ar yankin, amma abin haushi da takaici banda Arewacin Nijeriya.

Idan ana batun ci gaba a duniya ta fannoni daban-daban, to haƙiƙa ƙasashen duniya sun yi nisa, kuma sun yi wa Nijeriya fintinkau, hatta da nahiyar Afurika akwai ƙasashe da dama da suka ɗara Nijeriya, wanda a da can ko kama ƙafar Nijeriya ba su yi ba a kowacce fuska, amma a yau Nijeriya ta koma baya sosai a kan ci gabansu da suka samu.

A baya-bayan nan mun ga yadda wasu shugabanni uku daga cikin shugabannin ƙasashen Afurika da suka fice daga ƙungiyar (ECOWAS), shugaban ƙasar Nijar, shugaban ƙasar Mali da Burkina Faso. Waɗannan shugabannin ƙasashen uku dukkansu shugabannin mulkin soja ne da suka yi juyin mulki a hannun farar hula, wanda hakan ya faru ne a bisa dalilin rashin tsaro, satar kuɗin ƙasa da wasu abubuwa marasa daɗi da suka haifar da rashin aikin yi ga ‘yan ƙasa tare da rashin kwanciyar hankali sakamakon aikin ta’addanci da ake yi a ƙasashen.

Duk da cewa a baya mun ga irin yadda ita ƙungiyar (ECOWAS) ta riƙa yin barazana da saka takunkumi ga ƙasar Nijar sakamakon juyin mulki da sojoji suka yi, ƙarƙashin shugaban mulkin soja na yanzu Abdurrahman Jani, amma dai a ƙarshe yau an wayi gari shi da takwarorinsa na Burkina Faso da Mali sun fice daga cikin wannan ƙungiya. Wannan shi zai nuna mana cewa, ko shakka babu waɗannan shugabanni suna kishin ƙasarsu, haka nan kuma suna kishin al’ummar ƙasarsu.

Sun nuna damuwa a kan rashin tsaro, sun kuma ɗauki matakin kawo ƙarshen matsalolin da suka addabi, ko neman addabar ƙasashensu, ta hanyar haɗa kai tare da gama hannu da kafaɗa don kakkave ɓata gari da nufin samar da kyakkyawar makoma ga al’umma da ci gaban ƙasa.

Kamar yadda na faɗa cewa Arewacin Nijeriya shi ne babban tushen ci gaban Nijeriya, shi ne tushen ginuwar Nijeriya, kuma shi ne babban tubali da ya kamata a ce an kula da ginshiƙansa ta fuskar raya ƙasa da al’ummar ƙasa, wanda kuma alhakin hakan ya rataya ne ga jagororin al’umma da suke jan ragamar ƙasa a hannunsu, amma manyan Arewa sun yi watsi da Arewa, ba su damu da yankin Arewar ba, hakazalika ba su damu da al’ummar Arewar ba. Saɓanin hakan sun gwammace su siyasantar da al’amura ta kowacce fuska, ta yadda kullum za a yi bajat a kasafta kuɗin ƙasa da al’ummar ƙasa a wawure a bar talaka da hamma.

Mu kalli lokacin da tsohuwar Gwamnatin Buhari ta samu ikon jan ragamar wannan ƙasa, aka raba muƙamai masu tarin yawa ga ‘yan Arewa, har ta kai abokanan zamanmu dake ɓangaren kudu suna ganin kamar an yi son kai wajen rabon muƙamai, amma a madadin ‘yan Arewa su taimaki gwamnatin Buhari don a gina ƙasa, a ciyar da ƙasa gaba, sai kawai ya kasance sun yi shakulatin vangaro da yankin, suka yi ta badan-badamarsu da sharholiya har gwamnatin ta ƙare.

Yau ga shi zuwan wannan sabuwar gwamnatin tun ba a je ko’ina ba an ga irin salon mulkin da ta zo da shi, wanda za a iya cewa ana fifita wani vangare a kan wani. To amma wannan ba shi zai sa a ga laifin shugaban da ke ci a yanzu ba, illa iyaka mu kalli rashin kishi da sanin ciwon kai da manyanmu na Arewa suke dashi. Domin da suna kishin al’ummar yankin da shi kansa yankin, da tun lokutan baya ya kamata a ga kishin a wajensu da kuma cikin al’umma da yankunan da suke shugabanta yake.

Idan ana maganar rinjayen shugabanci da ƙarfin iko na madafu da kuɗi a Nijeriya yankin Arewa ake kira, idan ana batun kasuwanci da tattalin arziki a Nijeriya duk yankin Arewa ake tunƙaho da shi, dalili kuwa shi ne, saboda yankin Arewa ne ake da babbar ƙasar noma a Nijeriya da duk abinda aka shuka shi a gonaki zai haɓɓaka ya samar da abinci, haka nan kuma idan kasuwanci ne hatta mutanen kudu nan ne wajen tinƙaho da tushen bunƙasa kasuwancinsu da suke tutiya da shi.

Kasuwannin Arewa kaf! Babu inda za ka je ba ka samu Inyamiri da Bayarabe ba, ko wasu ƙabilu da suke kudu amma suna zaune a Arewa suna kasuwanci kuma sun zama manyan masu kuɗi ta dalilin kasuwanci, babu kuma wani ɗan Arewa da yake fitowa ya nuna zai yaqi ƙabilun kudu da suke kasuwanci a Arewa don sun tara dukiya ko kadarori. To amma a kudu babu wani Bahaushe ɗan Arewa, ko wata ƙabila daban da ta fito daga Arewa ta je kudu ta samu matsugunni mai kyau don kafa tushen  sana’a ba tare da an nuna ƙabilanci ba.

Yau a Arewa duk da cewa muna da manyan mutane, jagororin al’umma da suke nuna sun isa suna faɗa aji, amma ana cikin ƙuncin rayuwa na tashin hankali da rashin kwanciyar hankali da aka jima a ciki ba su yi wani abu da zai kawo ƙarshen matsalar ba, ana kashe-kashen jama’a da satar mutane a nemi kuɗin fansa, wannan ma an yi kurum an kau da kai kullum sai ƙara gaba abu yake yi babu ranar ko alamun za a bari, cin hanci da rashawa, rashin daidaitaccen farashin kayayyaki a kasuwanni, rashin aikin yi, ƙarancin albashi, tsadar man fetur da gas, tsadar kayan masarufi da sauransu. Duk wannan abubuwan ɗaya zuwa biyu ne a cikinsu ba Arewa ake samar da shi ba, amma duk sauran a Arewa suke sai dai kuma ‘yan ƙasa suna shan wahala wajen samunsu don tafiyar da rayuwa.

Idan muka kalli ɓangaren muhalli da abin hawa da a da talaka yake samu ya mallaka a cikin sauƙi, kamar su; Babur, mota da keke don yin zirga-zirga zuwa wajen aiki ko kasuwa, a yau kuɗin Babur Lipan ko Jincan sai wane-da-wane, keken ma ba kowanne talaka mai rufin asiri ne zai iya mallaka ba saboda tsananin rayuwa da tsadar da komai ya yi. Wannan bai damu manyan Arewa ba, ba kuma shi ne a gabansu ba.

Duk kashe-kashen da ake yi na al’umma, da ɗaukar mutane a nemi kuɗin fansa, hakan ba ya zame musu abinda zai iya hana su barci a kan yadda suke kasa yin bacci idan aka zo batun zaɓe, ko raba muƙaman siyasa a gwamnati ba. Duk lokacin da aka buga kogin siyasa to wannan lokacin duk wani abu da suke yi hankalinsu na kan siyasarsu ne kurum, haka nan idan aka zo rabon muƙaman siyasa ma ba sa ta talakawa, ba sa ta halin da ake ciki, kawai sha’anin gabansu da abinda suke cimma wa shi suke mai da hankali a kai.

Manyanmu na Arewa sun kau da kansu daga barin al’ummar Arewa, sun kau da kansu a kan duk wani farin ciki da jin daɗi da za su saka hannu a kan shi domin walwala da annushuwa su samu talakawan Nijeriya, saɓanin hakan sun fi ƙoƙari a lokacin (Campaign) su zubo kuɗi a aljihu da katan-katan ɗin taliya, da sabulai masu ɗauke da hotonsu a kwali, ko gidan sauro, da omo da manshafa su zo suna bi unguwa-unguwa suna raba wa marasa galihu don kawai a kaɗa musu ƙuri’a, daga ranar da kuma suka ci shi kenan kai da su sai dai idan wani lokacin zaɓen ya dawo su ƙara dawowa gare ka.

A yau dai mun riga mun gani cewa, manyan Arewa sun ɗauke kansu daga kan duk wani tashin hankali da masifa ta tsadar rayuwa ko wanin haka da talaka yake ciki, kullum al’amura ƙara gurɓacewa suke yi, abun babu kyau babu kyan gani, babu tsari, babu doka, babu wata alama ta kawo ƙarshen halin da ake ciki na fatara, yunwa da talauci da ya dabaibaye al’umma.

Ma’aikacin Gwamnati yana aiki a ma’aikatar gwamnati, yana zaune a gidan haya, ga iyali, ga abincin da za a ci, kuɗin wutar lantarki, sayen magani a asibiti, kuɗin karatun yara da sauransu, amma a wata bai fi ya samu Naira dubu (30) ba. Ta ina dubu talatin a wannan zamanin za ta ishi ma’aikacin gwamnatin da a ƙalla yana da mace ɗaya da yara huɗu ko biyar, suna makarantar kuɗi ko ta gwamnati, buhun shinkafarmu ta gida ma da ake gyarawa a zuba a buhu kamar ta waje ta kai Naira (58,000) dubu hamsin da takwas? Manja da man gyaɗa kwalba wanda a da Naira (350) yanzu dubu da ɗari biyu (1,200)? sukari Naira (4,200) kwano, masara (1,200) kwano, dawa, gero duk sun yi tsada.

Ina hankalin manyan Arewa yake ne? shin a Nijeriya suke rayuwa ko kuwa a ƙasar Dubai, Ingila ko America da ba za su fahimci halin da ‘yan ƙasa suke ciki ba su tashi tsaye don ganin sun yi abinda ya dace? Wannan shi yake tabbatar mana da cewa manyan Arewa sun kassara ci gaban al’umma da yankin Arewa ne da gangan, da wata manufa tasu ta ɗauke kai don samun wasu abubuwa na buƙatunsu da iyalansu kaɗai, domin kuwa sun riga sun san cewa ‘ya’yansu sun tara masu dukiyar da ko da bayan ransu ba za su tagayyara ba.

Ya kamata manyanmu na Arewa ku dubi Allah da girmansa, ku dubi halin da al’ummar Nijeriya muke ciki na fatara, yunwa da talauci da ya yi wa mafi yawan al’ummar Nijeriya da Arewa kamun kazar kuku, ake ta fagamniya da faɗi tashin rayuwa cikin zufa da ƙugin hanji, da kwana da yunwa, da ƙwace da ƙarfi da tare hanya.

Dukkan waɗannan ayyukan suna faruwa ne a dalilin rashin aikin yi, da yin amfani da ƙwaya don samun nutsuwar ƙwaƙwalwa (musamman ga matasa maza da mata), me ya sa duk manyanmu na Arewa ba za ku kalli wannan al’amarin ku yi yadda ƙasarmu Nijeriya da yankinmu na Arewa za su dawo cikin hayyacinsu ba? Kullum Dalar Amurka a kasuwar canji tashi take ƙara yi a Nijeriya, yayin da darajar Nairarmu take ƙara yin ƙasa tana lalacewa, wanda hakan ke ƙara haifar da koma baya a kan harkokin kasuwanci da saye-da-sayarwa. Shin ba za kuyi kishin wannan ba ku fitar da al’umma cikin ƙunci?

Mu kalli yadda mata suka kasa samun kulawa daga wajen mazajensu, wataƙila mazan sunyi iyakar yinsu a lokacin da rayuwar take da sauƙi, amma kuma a yanzu da al’amura suka rincave ta kai ta kawo mazan suna ƙulle kayansu su gudu su bar mata da yara su shiga uwa duniya saboda zafin babu, wani ba mutuwa ya yi ba amma saboda masifa ko ɗuriyarsa ba ya bari aji, wani kuma zuciyarsa ce za ta buga ya mutu, wani kuma rataye kansa zai yi, wani yana tafe yana tunanin halin babu mota ta kaɗe shi, ko mashin ya buge shi a sakamakon tunanin da yake yi na halin rayuwa.

Idan har ya tabbata muna da manya a Arewa, kuma sun yarda su wakilan jama’ar Arewa ne, to ya kamata su sa kishin Arewa da al’ummar Arewa da ma Nijeriya gabaɗaya a cikin zuciyarsu, domin duk ɗan Nijeriya ba shi da wata ƙasar da yake alfahari da ita da tinƙaho kamar Nijeria, to kenan kuma me ya dace jagorori su yi? Don haka a yi duba na tsanaki dangane da wannan al’amari.

Nafi’u Salisu,
Marubuci/manazarci,
imel: [email protected], [email protected]
08038981211, 09056507471. Ya rubuto daga Kano, Nijeriya