Hauhawar farashi laifin wa? Taron CO28 ya zo da bazata

Tare da BASHIR MUDI YAKASAI

“Ita karya fure ta ke yi, amma ba ta ’ya’ya, amma a daka, a raya sai gaskiya”, haka ma’abota hankali suka tabbatar wa al’umar duniya. Mai karatu mun yi wannan Ambato ne domin mu jawo hankalinka ne, me ya sa daga janye tallafin man fetur a kasannan shikenan sai farashin kayayyakin masarufi sai tashin gwauron zabi yake yi babu kakkautawa.

Wani abin takaici duk bayan sa’a guda sai kaji farashin kaza ya karu babu gaira babu dalili. Kuma idan k nemi ba’asi sai a ce maka dalar Amurka ce ta tashi a kasuwar duniya. Idan ka yi tambaya me ya hada shinkafar da aka noma a gida Nijeriya kuma aka sarrafata a gida Nijeriya ta yaya farashin ya hadu da dalar Amurka?

A shekarun baya abin da muka sani wajan tashin farashin kaya shine ƙarancin kaya ko kuma rashinsa a kasuwa shi yake bayyana hawa da sauka na farashin kaya. Wannan shi ya haifar da kka a duk ƙarshen kowcce dmin, a lokacin kaya yake saukowa domin a kwai shi a kasuwa mai tarin yawa.

A wannan lokacin ‘yan kasuwa marasa Imani, saisu shigo kasuwa su saye amfanin gona, musamman abinci kamar Dawa, Gero, Maiwa, Masara, Shinkafa da kuma Alkama sai rani yayi rani kaya yayi karanci sannan zasu fito da kayan da suka saye kuma suka ɓoye a rumbuna da store-store, su sayar a farashi mai tsada. Wannan ts gwmntocin baya suka zo da hakuman nan ta “Marketing Board” wacce take kula da farashin kayayyakin masarufi a kasa. Duk wanda ya karya farashi sai a hakuntashi.

A wannan shekaru, ita ma gwamnati na sayen kyn masarufi ta ajiye a rumbunta saboda ko ta kwana, sai ta fito danata kayan ta kai kasuwa domin ta hana tashin farashin kaya. Bugu da kari baby wanda yake ciniki da kudin wata kasa, wai ita Amurka ko Dalar ta. Tambayar ta mu ita ce, wayake da alhakin tayar da farashi kaya ne? ko kuma wasu mutane a bayan kasuwa su suke d alhakin yin farashi hwansa da saukarsa?

Ciniki d kuɗin wata ƙasa ko da kuwa maƙociyar k ace haramun ne, balle wata ƙasa da kuke nesa da juna kamar Amurka ta Arewa wato USA. Koda kuwa a lokacin mulkin mallaka, ko wacce ƙasa da nata kudin, amma a wannan ƙarni na 21, haka kawai su ba hakuma ba, amma su za su riƙe ragamar kasuwanci a ƙasa. Idan ka tambaye su wacce hajja suke da ita a kasuwa? Amsa shine babu.

Wani abin mamaki dana gani a kasuwar garin mu masu syar da Goriba da Aduwa da Agwalima da magarya zan sayawa yara da mai dakina tsaraba, abin mamaki sai aka ce farashin ya sauya daga gwan da na sani na Aduwa da Magarya Naira goma (₦10) sai aka ce mun farashi ya koma Naira sittin (₦60) na Aduwa, kuma Naira casa’in (₦90) na magarya. Ita kuma Goriba da muke saye guda biyar (5) zuwa bakwai (7) na Naira goma (₦10), yanzu duk guda daya ta koma Naira Ashirin (₦20). Agwaluma ta zama ‘yar sarki domin ko wace ɗaya ta koma Naira hamsin (₦50).

Dana tambayi ba’asi sai aka ce mun ba ni da labarin tashin dala kasuwa? Sai wani daga cikin ‘yan kasuwa ya ce mun, kai ba ɗan Nijeriya ba ne ko? Kuma baka da labarin “subsidy removal” cire tallafi da shugaban kasa ya yi akan man fetur? Nan take na mayar da tambaya me ya hada cinikin Goruba da Magarya da Aduwa da kuma agwaluma da cire tallafin man fetur? Nan take kuwa aka bani amsa, da cewa kuɗin dakon kaya ga kuma rufe boda a iyakarmu da ƙasar Nijar.

Me karatu, kaji wata kwanr sama da kuma raina hankali, amma maganar gaskiya, wannan sakaci ne na gwamnati da ta ƙyale wasu wawaye (stupids) suna tafiyar da ƙasar nan ta hanyar wawanci (stupidity). Haka kawai, wasu barayin zaune da sunan kasuwanci suna azabtar da ‘yan ƙasa inda suke asara rayunkansu ta hannun mutanan da ba su kai kashi ɗaya cikin ɗari na ‘yan ƙasar nan ba, amma ana kallo su an ƙyale su.

Shugaban Ƙasa Asuwaju Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa Kashim Shatima Mustapha ya zama wajibi a gare ku da ku yaki wannan mummunar ɗabi’a ku kawar da duk wata kafa da wasu masu ci da gumin ‘yan Nijeriya ‘yan ƙalilan, yin haka in tabbatar muku zaku ci zaɓe a shekara ta 2027 da 2031 da kuma shekara ta 2035. Kada kuji tsoran su, ‘yan Nijeriya na tare daku idan har kuka kawar da su daga doran ƙasa. Doka maitsananin gaske kota kai da kisa ‘yan Nijeriya za su dafa muku.

Bola Tinubu ka yi rawar gani da ka soke tallafin man fetur wanda Janar-Janar kamar, janar Ibrahim Badamasi banagida da janar Sani Abacha da janar Abdulsalami Abubakar da kuma Janar (Chief) Olusegun Obasanjo suka kasa, saboda kawai suna jin tsoron su, kai kadai ba tare da shawara da kowa ba, kuma abin yayi. Kamar yadda muka ce ku daura yaki da wannan wawaye, ku tabbatar kun kai su ƙasa, koda kuwa daga ina suke samun ɗaurin gindi, komai girman su.

Babu wani dalili tartibi da zai sa kayan masarufi da ake buƙata yau da kullum musamman abinci da muke noma a ƙasar nan wasu tsiraru su zasu ce ga yadda za a siyar da sunan dola ko yero koma saifa. Bola Ahmed Yinubu da mataimakinka Kashim Shatima Mustapha, Allah ya baku, kuma kun yi Imani da rananr gobe kiyama, to tsoran wa kuke Amurka da Kawayenta – Birtaniya ko Faransa ko kuma Jamus dukkan su Balanbalan ne, kuma cewa kun ƙi, ba ku yard aba, zaku sace su, sacewar da zata kai su ƙasa wanwar.

Bola Tinubu da Kashim Shatima na san kun sani Nijeriya ta fuce, Nijeriya ta 1960 a duk wani fanni na rayuwa – Ilimi, Noma da kiwo, masana’antu sarrafa makamashi ma’adanai da kuma karfin wutar lantarki (energy, solid, mineral & power) abin da ake bukata matanan da za su tsaya tsayin daka da za su yaki duk nau’in mrs gaskiya a duk inda suke a wannan sarari na subahana.

Duk fadin Afirka da kasashe sama da hamsin babu ɗaya kacokan da sukafi ƙarfin yunwa da talauci da cututtuka da kuma zaman lafiya a ƙididdiga da kuma bincike da hukumar kuɗi ta duniya (IMF) ta gudnar a shekara da ta gabata – 2023, babu kasa daya tak daga Afirika daga matakin na daya zuwa na goma bisa sikelin da aka dora kasashe su 237 na duniya, amma abin kunya babu Nijeriya, babu Afirka ta kudu, babu Misira (Egypt).

Dalilan da aka ce sune suka sa ƙasashe goma har d Denmark da Aurtalia da Iceland da Amurka da Singapore da Norway da Qatar da Switzerland da Ireland da kuma Luxembourg aka nuna sun yi shura shine abubuwan da Nijeriya take da su kamar yadda muka ambata a baya, amma matsalarmu ita ce ta shugabanci – wato faɗa da cikawa kamar yadda Bila Ahmad Tinubu yayi dangane da cire tallafin man fetur. Haka, Tinubu da Shatima za su iya yakar ma’abuta Dala, domin kuwa babu abin da ya hadamu da Dala, illa cinikin ƙasa da ƙasa, idan muka ce mun daina da Dala, sai me?