Daga BASHIR ISAH
Shugaban Kasa Bola Tinubu ya bai wa Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara a Harkar Tsaro (NSA), Nuhu Ribadu da IGP Kayode Egbetokun da Daraktan DSS, Yusuf Bichi umarni kan su yi aiki tare da gwamnoni wajen yaki da masu boye abinci a kasa.
Kafin wannan umarnin na Shugaba Tinubu, ‘yan Nijeriya na fama da karancin abinci ba wai don babu abincin ba, sai don wasu ‘yan kasuwa sun tara abincin sun boye wanda hakan ya haifar da tsadar kayan abinci a sassan kasar.
Sai dai a wani yunkuri da gwamnatin kasar ta yi don yaki da wannan hali na bnoye abinci, Ministan Labarai da Wayar da Kan ‘Yan Kasa, Mohammed Idris, ya ce Tinubu ya umarci hukumomin tsaro da NSA kan su yi aiki tare da gwamnoni wajen kawar da wannan mummunar al’ada.
Idris ya ce, “Da farko, an bai wa Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara a Harkar Tsaro da Babban Sufeton ‘Yan Sanda da Daraktan DSS, umarni kan su hada hannu da gwamnonin jihohi wajen yaki da masu boye kayan abinci”.
Ya bayyana hakan ne bayan ganawa da Shugaba Tinubu a ranar Alhamis a Abuja.
Ya kara da cewa, “A daidai wannan lokaci da ake bukata a fito da kayan abinci domin mu samu mu daidaita farashi don amfanin ‘yan kasa, a lokacin ne kuma ‘yan kasuwa suka bada himma wajen boye abincin don wahalar da ‘yan kasa ko kuma don neman kazamar riba.
“Don haka gwamnoni da Shugaban Kasa sun yi matsaya kan cewa hukumomin tsaro su hada kai da gwamnoni wajen kawo karshen lamarin.
“Domin amfanin ‘yan kasa, an yanke shawarar babu bukatar shigo da abinci daga ketare a daidai wannan loakaci. Nijeriya na da karfin da za ta ciyar da kanta har ta kai ketare.”
Daga nan, Idris ya ce tsadar rayuwar da ake fuskanta yanzu na dan lokaci, don haka ya bukaci ‘yan Nijeriya a kara hakuri saboda a cewarsa, lamarin zai zama labari nan ba da dadewa ba.
