Hukumar Zaɓe ta Katsina ta sanar da ranar gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi

Daga UMAR GARBA a Katsina

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Katsina (KATSIEC) ta saka ranar 15 ga watan Fabrairu, 2025 a matsayin ranar gudanar da zaɓukan shugabannin ƙananan hukumomi da kansilolo a jihar.

Shugaban hukumar, Lawal Alhassan Faskari ne ya bayyana haka a wurin taron masu ruwa da tsaki kan zaɓen wanda ya gudana a hedikwatar hukumar dake G.R.A.

A cewar shi, jam’iyyu masu rajista ne kawai za a bari su tsayar da ‘yan takara a kujeru daban-daban.

Alhaji Lawal Alhassan ya ce sashe na 28 na dokar zaɓen Nijeriya da aka yi wa gyaran fuska 2022 ne ya tanadi cewa a sanar da zaɓen kwanaki 365 gabanin gudanar da shi.

Ya ƙara da cewa nan gaba za su raba takardun da ke ƙunshe da ƙa’idoji da dokoki da kuma tsare-tsaren zaɓen.

“Dukkan masu sha’awar tsayawa takara da suka cancanta daga jam’iyyun siyasa masu rijista za su iya tsayar da ‘yan takara a muƙamin chayamomi da kansiloli bayan sun cika dukkan sharuɗɗan takarar.

” Yan takarar da jam’iyya ta ɗauki nauyinsu ne kawai za a bari su shiga zaɓen.” Inji shi.

Ya yi kira ga jami’an tsaron jihar akan su samar da tsaro lokacin gudanar da zaɓen musamman ƙananan hukumomin dake fuskantar matsalar tsaro.