Kano: An yi wa ‘yan marasa galihu 16 auren gata a Bichi – Kwamandan Hisbah

Spread the love

A karo na biyu da Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ke gwangwaje mata marasa ƙarfi da auren gata a ƙarƙashin Hukumar Hisba, ‘yan mata guda 16 za su rabauta da irin wannan aure a Ƙaramar Hukumar Bichi.

Kwamandan Hisba na yankin, Malam Murtala Safiyanu ne ya bayyana haka a yayin tattaunarwasu da Jami’ar Yaɗa Labarai ta yankin, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo a ofishinsa dake Cibiyar adinin Musulunci ta ƙaramar hukumar.

Ya ce, kayan da gwamnati ke ɗaukar nauyin bayarwa kama daga setin gado zuwa kayan abinci na gara, tuni Gwamna Abba Kabir Yusuf ya cika alƙawari, inda Ƙaramar Hukumar Bichi su ma aka kai musu nasu domin tabbatar da haɗa wannan babbar sunnah. Kazalika ya shaida kayan ɗakin a matakin matsayi da ingancin da ba a taɓa yin kamarsu ba.

“Shinkafa, taliya, makaroni, mai, katifu, filoli, zannuwan gado, ledar ɗaki, kayan sawa atamfofi da shaddodi yadi 10-10 na ankon amare da angwaye da mayafai da huluna duk suna hannu, kawai ɗaurin aure muke jira da za a yi 7 ga watan gaba tare da walima a gidan gwamnati in sha Allah. ” Malam Murtala Safiyanu.

kwamandan ya ƙara da cewa, a yanzu dai yadda ake gudanar da Auren Gata da Gwamna ke yi ƙarƙashin hukumar ta Hisba, ya sha bamban da yadda aka sani a baya, wanda haƙiƙanin cancanta a yanzu kaɗai ke tasiri a cikin al’amarin, sannan ya bayyana ‘yanmata ne kaɗai suka rabauta a wannan karon bisa la’akari da auren budurwa ya fi kashe kuɗi.

“Fama-famai da ake rabawa mazaɓa-mazaɓa; haƙƙin al’umma ne tun daga kan dagaci zuwa ƙasa su duba wanda ya fi tsananin buƙata a ba shi, misali a wata mazaɓa akwai wani bawan Allah da aka sa auren ‘yarsa sau 3-4 ana ɗagawa saboda rashin sukuni, amma cikin ikon Allah yanzu sun shiga cikin wannan tsarin.

Muna godiya ga mai girma Gwamna tare da babban Kwamandan Hisbah Sheikh Malam Aminu Ibrahim Daurawa bisa ƙoƙari da jajircewa wajen tabbatar da wannan al’amari na alheri.” Malam Murtala Safiyanu.

Ya kuma yi godiya ga Shugaban Majalisar ƙaramar hukumar Alhaji Hamza Sule Maifata bisa bayar da goyon bayan yadda za a gudanar da lamarin yadda yakamata na tabbatar da adalci a kafatanin yankin.

By Babaji

Leave a Reply