Hukumar bogi: Shugabar Ma’aikata ta je gaban kwamitin majalisa yayin da Sufeto-Janar ya gaza kai Adeyemi kan hukuncin kotu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Laraba kwamitin wucin-gadi na Majalisar Wakilai da ke gudanar da bincike akan zargin hukumar kula da inganta zuba jarin ƙasashen waje ta shugaban ƙasa (PFIPC) ya sanar da takardar ɗaukar aiki ta wanda ya kira kansa da darakta janar ɗinta, Mista Adeniyi Adeyemi, a matsayin ta bogi duk da cewa Rundunar ‘Yan sandan Nijeriya ba ta gabatar da shi ba a gaban kwamitin kamar yadda ya umarta.

Akan haka ne wakilan ‘yan sanda suka shaida wa kwamitin cewa suna buƙatar rubutaccen umarni daga kotu da zai ba su izinin fitar da Adeyemi kafin su bi umarnin majalisar.

A ranar Litinin ne kwamitin, ƙarƙashin jagorancin Ɗan majalisa Yusuf Gagdi (APC, Filato) ya umarci Sufeto-Janar na ‘yan Sanda, Olatunji Disu da ya gabatar da Adeyemi a gabansa kafin ƙarfe 12 na ranar Laraba domin taimaka wa binciken da ake gudanarwa kan al’amarin.

Sai dai a lokacin da kwamitin ya sake zama, jami’an ‘yan sanda sun bayyana wa kwamitin cewa ana tsare da Adeyemi ne bisa umarnin kotu na a cigaba da tsare shi, don haka ba za su iya kawo shi gaban kwamitin ba sai da sahalewar kotu.

Haka kuma, ‘yan sandan sun ce har yanzu suna da niyyar bayar da cikakken haɗin kai ga binciken da majalisar ke gudanarwa, amma wajibi ne su tabbatar da cewa sun kiyaye umarnin kwamitin da bai saɓa wa na kotu ba.

Shugaban kwamitin, Yusuf Gagdi ya bayyana cewa, Shugabar Ma’aikatar Ma’aikata, Misis Esther Wilson-Jack, wadda ta je gaban kwamitin a karo na biyu, ta tabbatar da cewa takardun da Adeyemi ya gabatar ba sahihai ba ne.

Wilson-Jack ta hallar a gaban kwamitin ne bisa biyayya ga gayyata da aka mata da fari domin bayar da cikakken ba’asinta akan al’amarin.

By Babaji

Leave a Reply