Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Kwamintin da gwamnatin Jihar Katsina ta kafa na tantance ma’aikatan ƙananan hukumomi 34 da ke jihar ta fara tantance masu ƙorafe-ƙorafe.
Ma’aikata da dama da basu sami tsallake tantancewa ba suka miƙa takardar ƙorafe-ƙorafe wanda yasa gwamna Dikko Raɗɗa ya umarci kwamintin da ya sake duba koken su.
Kwamintin ƙarƙashin shugaban mai ba gwamna shawara kan ƙananan hukumomi Alhaji Lawal Rufa’i Safana ya fara da ma’aikatan ƙananan hukumomin Kaita,Batagarawa da Katsina.
Kwamintin ya fara da ma’aikata 100 da suka fito da ga waɗannan ƙananan hukumomin inda zai sake duba takardar karatu da na ɗaukar aiki ,su kuma bincika su tabbatar da sahihancin sa.
Ba da ɗaɗewa ba shugaban kwamintin ya miƙa rahoton kwamintin bayan duba takardar ƙorafe-ƙorafe har guda 900 da ma’aikatan da suka ƙasa tsallake tantancewa wanda shine kwamintin yake sake tantance su.
Tantancewar shine zai bada samar biyan albashi da sauran alawus na ma’aikatan da suka sami nasarar tantancewa.
Kwanan baya, gwamnatin jihar ta ƙaddamar da kwamintin tantance ma’aikatan ƙananan hukumomi 34 na Jihar inda ma’aikata 3000 suka kasa tsallakewa.
