
Rundunar Sojin Nijeriya ta ɗauki wani sabon mataki na ƙarfafa tsarin aikinta, bayan Babban Hafsan Sojojin Ƙasa (COAS), Laftanar Janar Waidi Shaibu ya amince da nadin sabbin Shugabannin Runduna (General Officers Commanding – GOCs) domin jagorantar sabbin rundunoni hudu da aka kafa.
Wannan sauyi ya biyo bayan amincewar Shugaba Bola Ahmed Tinubu na faɗaɗa tsarin rundunar sojin ƙasar daga runduna takwas zuwa runduna 12, tare da shirin ɗaukar sabbin jami’an soja 28,000 domin ƙara ƙarfin rundunar.
Sabbin naɗe-naɗen na daga cikin shirye-shiryen sake fasalin rundunar, inda aka kuma yi sauye-sauyen mukamai ga wasu manyan jami’an soja, ciki har da Brigadier Generals, domin tabbatar da samun ingantaccen shugabanci a sabbin sassan da aka ƙirƙira.
Rundunar ta ce wannan mataki na da nasaba da buƙatar ƙara inganta ayyukan tsaro da kuma tabbatar da cewa sojoji sun fi kusanci da wuraren da ke fuskantar matsalolin tsaro.
Masu sharhi kan harkokin tsaro sun bayyana cewa ƙarin rundunoni na iya taimakawa wajen saurin mayar da martani ga barazanar tsaro, musamman a yankunan da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga, ta’addanci da sauran ƙalubalen tsaro.
Sai dai masana sun jaddada cewa nasarar wannan sabon tsari za ta dogara ne da samar da isassun kayan aiki, horo na zamani, da kuma kyakkyawan tsarin gudanarwa domin tabbatar da cewa ƙarin rundunonin sun cimma manufar da aka tsara musu.
Faɗaɗa rundunar sojin Nijeriya na zuwa ne a wani lokaci da ƙasar ke ci gaba da neman sabbin hanyoyin magance matsalolin tsaro da suka shafi yankuna daban-daban.
