Daga AISHA ASAS
Mai karatu, barkanmu da sake saduwa a shafin Iyali na jaridar Blueprint Manhaja. A wannan mako za mu tattauna wani muhimmin batu da duk da girman tasirinsa ga rayuwar iyali, ba kasafai ake ba shi kulawar da ta dace ba, musamman a Arewacin Najeriya. Batu ne da ya shafi lafiyar ƙwaƙwalwa, musamman cutar damuwa (anɗiety) da kuma baƙin ciki mai tsanani (depression).
A gidaje da dama, akwai matsalolin da ba sa bayyana a ido, amma suna girgiza zaman lafiyar iyali. Cutar damuwa da baƙin ciki na daga cikin irin waɗannan matsaloli. Mutane da yawa na rayuwa da su ba tare da sun gane abin da ke damunsu ba, ko kuma saboda tsoron abin da jama’a za su faɗa. Sai dai, ko da iyaye ne ke fama da waɗannan matsaloli, yara ma ba sa tsira daga tasirinsu.
Ko da yaro bai san sunan cutar ba, sau da yawa yana iya fahimtar cewa wani abu ya sauya a cikin gida. Hakan na iya shafar tunaninsa, halayyarsa da kuma yadda yake kallon kansa da waɗanda ke kewaye da shi.
ɗaya daga cikin alamomin da yara suka fi saurin lura da su shi ne canjin halayen iyaye. Idan uwa ko uba sun fara yawan yin shiru, rashin magana, yawan kuka ko rashin jin daɗin abubuwan da a da suke faranta musu rai, yaro kan fahimci cewa akwai wata matsala, ko da ba zai iya bayyana ta da kalmomi ba.
A wasu lokuta, yaro kan ɗora wa kansa laifi. Yana iya tunanin shi ne ya jawo halin da iyayensa suke ciki. Wannan tunani kan hana shi samun kwanciyar hankali, har ya fara jin kamar ba a ƙaunarsa ko ba shi da wani muhimmanci a cikin iyali. Idan aka bar wannan yanayi ba tare da an kula da shi ba, zai iya haifar masa da wasu matsalolin tunani da na ɗabi’a yayin da yake girma.
Wane tasiri hakan kan yi ga halayen yaro?
Yaron da yake rayuwa a gidan da ɗaya daga cikin iyaye ke fama da cutar damuwa na iya fara nuna wasu sauye-sauye a halayensa. Zai iya zama mai yawan jin tsoro ko damuwa, ya fara ware kansa daga mutane, ko kuma ya daina son magana da kowa.
Wasu yara kuma kan zama masu saurin fushi, su riƙa nuna rashin haƙuri ko kuma su riƙa yin abubuwan da ba su dace ba saboda ba su iya bayyana abin da ke damunsu.
Haka kuma, yaro na iya daina sha’awar wasa da ‘yan uwansa ko abokansa, ya zaɓi zama shi kaɗai. Sau da yawa malamai ko maƙwabta kan yi zaton matsalar ɗabi’a ce kawai, alhali tushen matsalar na iya kasancewa halin da yake fuskanta a gida.
Wani tasirin da ake yawan gani shi ne koma bayan karatu. Yaro na iya ci gaba da zuwa makaranta, amma zuciyarsa tana cike da damuwa. Wannan yanayi kan hana shi mayar da hankali a aji, ya rage fahimtar darussa, har sakamakonsa ya fara raguwa.
A wasu lokuta ma, yaron kan fara ƙin zuwa makaranta gaba ɗaya. Idan ba a gano musabbabin hakan da wuri ba, yana iya shafar makomarsa ta ilimi da kuma rayuwarsa gaba ɗaya.
A wasu gidaje, musamman idan ɗaya daga cikin iyaye na fama da matsananciyar matsalar lafiyar ƙwaƙwalwa, yara kan tsinci kansu suna ɗaukar nauyin da bai dace da shekarunsu ba.
Su ne ke kula da ƙannensu, su dafa abinci, su yi wanke-wanke tare da tabbatar da cewa komai yana tafiya yadda ya kamata. Wannan nauyi kan hana yaro more yarintarsa, ya kuma sa ya girma cikin jin cewa ba ya da damar neman taimako ko bayyana damuwarsa.
Masana sun yi nuni da cewa irin wannan yanayi kan iya ci gaba da shafar mutum har zuwa lokacin da ya girma, musamman wajen yadda yake kallon kansa da kuma yadda yake hulɗa da sauran mutane.
ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da ake fuskanta a al’ummarmu shi ne yadda har yanzu ake kallon matsalolin lafiyar ƙwaƙwalwa. A wurare da dama, idan aka ce mutum na fama da wata matsalar lafiyar ƙwaƙwalwa, nan take wasu kan ɗauka cewa ana nufin “hauka”. Wannan kuskuren fahimta yana sa mutane da dama su ɓoye halin da suke ciki saboda tsoron abin da jama’a za su faɗa.
Sai dai yin shiru ba ya magance matsalar. A mafi yawan lokuta, shi ne ke ƙara tsananta ta, tare da barin yara suna rayuwa cikin yanayin da ba su fahimta ba. Saboda haka, kawar da kunya da kuma neman taimako cikin lokaci na daga cikin matakan farko na kare lafiyar iyali.
Shin ko akwai hanyoyin da za a rage tasirin matsalar ga yara?
Masana sun bayyana cewa akwai hanyoyi da dama da za su taimaka wajen rage tasirin cutar damuwa ga yara, musamman idan iyaye suka fara ɗaukar matakan neman taimako da wuri.
Na farko shi ne tattaunawa. Duk da irin yanayin da iyaye ke ciki, yana da muhimmanci su ci gaba da kusantar ‘ya’yansu tare da yi musu bayani cikin sauƙi, gwargwadon shekarunsu. Hakan na taimaka wa yara su fahimci cewa halin da suke gani ba laifinsu ba ne, kuma yana rage musu tsoro da ruɗani.
Haka kuma, amincewa da cewa akwai matsala wani muhimmin mataki ne na neman waraka. Idan mutum ya yarda da halin da yake ciki, hakan kan sauƙaƙa masa neman taimakon da ya dace.
Wata hanya kuma ita ce neman shawarar ƙwararrun ma’aikatan lafiya. Akwai likitoci da sauran ƙwararru da suka kware wajen kula da matsalolin lafiyar ƙwaƙwalwa. Su ne suka fi dacewa su tantance matsalar tare da ba da shawarwarin da suka dace kan magani da kuma yadda za a rage tasirin matsalar ga yara.
Daga ci gaban da aka samu kawowa yanzu, wasu makarantu na da malamai ko masu ba da shawara (counsellors) da ke kula da walwalar ɗalibai. Ko da yake irin wannan tsari ya fi samuwa a wasu makarantu masu zaman kansu, yana da amfani iyaye su sanar da irin waɗannan malamai halin da iyali ke ciki idan akwai buƙata. Hakan na ba su damar fahimtar sauye-sauyen da yaro ke nunawa tare da ba shi goyon bayan da ya dace a makaranta.
Baya ga haka, akwai ƙungiyoyi da cibiyoyi da ke ba iyaye da yaransu tallafi ta fuskar shawarwari, wayar da kai da kuma taimakon ƙwararru. Yin amfani da irin waɗannan damammaki na iya taimakawa iyali su shawo kan matsalar cikin sauƙi.
Dr. Miriam Ayele, ƙwararriyar likita mai kula da lafiyar yara, ta ce: “Yara na buƙatar su ji cewa ana ƙaunarsu, ana fahimtarsu, kuma ba su da laifi.”
A cewarta, idan iyaye suka samu goyon bayan da ya dace, hakan kan taimaka wajen kare yara daga illolin da matsalolin lafiyar ƙwaƙwalwa kan haifar a cikin iyali.
Duk da irin ƙalubalen da muka tattauna, kasancewar ɗaya daga cikin iyaye na fama da cutar damuwa ba yana nufin dole rayuwar yaro za ta lalace ba. Idan aka samu kulawa, fahimta da taimakon da ya dace, yaro na iya girma cikin ƙoshin lafiya, ya zama mai ƙwazo kuma mai iya gina kyakkyawar makoma.
Abin da ya fi muhimmanci shi ne kada a yi shiru ko a ji kunyar neman taimako. Gano matsalar da wuri da kuma ɗaukar matakan da suka dace na iya canza rayuwar iyali baki ɗaya.
Lafiyar ƙwaƙwalwa tana da muhimmanci kamar lafiyar jiki. Idan muka daina kallon matsalolin lafiyar ƙwaƙwalwa a matsayin abin kunya, muka buɗe ƙofofin tattaunawa tare da neman taimakon da ya dace, za mu taimaka wajen kare makomar yaranmu da kuma ƙarfafa zaman lafiyar iyalanmu.
