2027: Uba Sani ya ɗauki Jerry Adams a matsayin abokin tafiyarsa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna ya amince da ɗaukar Jerry Adams, wato Shugaban Hukumar Tattara Harajin jihar (KADIRS) a matsayin abokin tafiyarsa a zaɓen gwamnan 2027.

A wani rubutu da gwamnan ya wallafa a shafinsa na X ya ce ya ɗauki matakin ne bayan dogon nazari da addu’o’i, lamarin da ke nuna fita daga tsarin tikitin Musulmi da Musulmi da aka yi a 2019 da 2023.

A cewarsa, zaɓin ya nuna yadda gwamnatinsa ke ƙoƙarin ganin an kiyaye tsarin damawa da kowane ɓangare, gaskiya da adalci da kuma daidaito yayin gudanar da lamuran gwamnati.

Ya bayyana cewa, hana wani mataki ne na sake haɗa kan al’ummar jihar wajen cigaba da ƙoƙarin wanzar da zaman mai ɗorewa a tsakanin ‘ya’yanta.

Haka kuma, gwamnan ya bayyana Adams a matsayin jami’in gwamnati mai cike da ƙwarewa da aiki tuƙuru wajen sauke nauyin jagoranci musamman kan shugabancin KADIRS, inda wasu nasarori da dama da ya cimma suke nuna haka.

Masu sharhi na ganin wannan mataki ka iya sauya salon siyasar Kaduna musamman ganin yadda wasu ke ganin akwai rashin daidaito wajen zaɓar masu riƙe da madafun ikon jihar, inda yanzu gwamnan sauya matsaya don maslahar al’umma.

By Babaji

Leave a Reply