Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Sam Shehu Mujaddadi bai ƙwace ƙasar kowa ba, hasalima waɗanda su ka karɓi tuta ‘yan asalin yankin da su ke sarauta ne. Shehu Mujaddadi Bagobiri ne ko ɗan Gobir a matsayin mahaifarsa a ƙasarsa ta gado
Wallahi akwai takaici da ban mamaki wani dan kwangilar AIFOB ko na makiya Arewa wanda ba shi ma da alaƙa ta kusa ko nesa da Hausawa; ya rubuta wai Shehu Mujaddadi ya ƙwace ƙasar Hausa ko ya yaƙi wani Sarki da sauran shirmen makirci da sai a soshiyal midiya dandalin bulus na Bello Badum a ke gani.
In ka deɓe ƙasar Gobir inda shi ma Shehu ɗan yankin ne, ba wasu wajaje da ya taka da kafarsa. Allah cikin ikonsa da’awarsa ta kai nisan inda ƙafarsa ba ta taɓa takawa ba. Hatta Gobir ɗin ma Wallahi Sarki Yunfa ne ya yi yunƙurin kisan g!lla ga Shehu, da hakan ya sa Shehu kare kansa. In ba haka ba ai Shehu karantarwa ne kawai ya sa a gaba.
MASOYA NE SU KA TAFI WAJEN SHEHU DON KARɓO TUTA
Mu ɗau misalai a gurguje Sarkin Katsina na farko lokacin tajdidin Shehu shi ne Malam Ummarun Dallaje wanda a ka haifa a Dallaje daf da Katsina kuma asalin iyayensa daga masarautar Kanen-Bornu su ka taho inda tushensu ma Larabawa ne na masarautar Wadai a Chadi amma wannan yarfen na JIHADIN FULANI ya sa a ke cewa Sarkin Fulani na farko na Katsina.
Sarkin Kano na farko lokacin tajdidi Malam Sulaimanu ma a Kano a ka haife shi kuma zuriyarsu ta Mundubawa sun daɗe a Kano kuma kula da ilimi da tsoron Allah ya sa a ka nada shi sarautar Kano inda bai bar dukiya ba a lokacin da ya rasu a 1819 kuma bai ma ambaci wanda zai gaje shi ba don koyarwa ce a gabansa. Nan a ka samu gidan Dabo su ka shigo sarauta inda daga nan a ka samu laƙabin Kanon Dabo.
Malam Musa da ya zama Sarkin Zazzau na farko zamanin tajididi ma ɗan asalin Zazzau ne daga zuri’ar Mallawa kuma shi ya tashi ya tafi don mara baya ga aikin raya Musulunci na Shehu.
WAJE MA DA KASAR HAUSA
In mun duba Modibbo Bubayaro ma mai Gombe ai bai taɓa rayuwa a Gombe ta yanzu ba kuma hasalima a yankin Adamawa a ka haife shi inda don ƙaunar tajdidi ya tafi wajen Shehu ya karbo tuta. Hakanan Malam Yakubu na Bauchi ya karɓo tuta kuma bai kwace kasar kowa ba. Shi ya kafa Bauchi kuma har yanzu zuriyarsa ke sarautar masarautar.
Gaskiyar abun da ya faru malamai ne masu kaunar tauhidi su ka samu labarin fitowar Shehu a farkon ƙarni na 19 inda su ka yi tattaki daga yankunansu, su ka kai ma sa mubaya’a su ka kuma dawo sassan da su ka cigaba da koyarwa. Duk mai ƙaunar tajdidi kuma mai ilimin addinin Musulunci ko almajiri/ɗalibin ilimi ka iya samun addu’ar Shehu don ya tafi ya cigaba da karantarwa. Shehu iya nan Gobir ya zauna kuma ya rasu a nan garinsa a Sokoto da nan ma asalin ƙasar Gobir ne kuma shi ma haifaffen Gobir ne gaba da baya. Don an haifi Shehu a yankin Gobir a 1754 ya kuma rasu a yankin Gobir a 1817 a ka kuma yi ma sa kabari a nan yankin kuma har yau ɗin nan a nan ya ke.
Dududu Shehu ya yi kimanin shekaru 63 ne a duniya. Duk surutun nan da a ke yi Shehu bai bar dukiya fiye da littattafan addini da ya wallafa don amfanin Musulmin duniya ba. Makiya Shehu na yin hakan ne don kiyayya ga musulunci. Haƙiƙa da Turawa su ka zo don yaɗa addininsu, ba su ci bulus ba don sun samu Shehu ya kafa TAUHIDI kyam don haka su ka je gefen Daula su ka gama yayata muradunsu su ka koma a 1960. Haba in da Yammawa sun shiga Arewa sun same ta sakaka ai da yau wani labarin a ke yi. Matsafa, mushurkai da ‘yan daudu ba za su taɓa son Shehu ba. Ai yanzu kun fahimci dalilin.
SAM SHEHU MUJADDADI BAI KWACE ƙASAR HAUSA BA DON HASALIMA BAI TAɓA RANGAɗI A KO INA BA
IN BAN DA TURAWA MA DA SU KA ɗAU IYA MUƙAMIN SULTAN, SHEHU JAGORANCIN ADDINI YA GADAR “AMIRAL MUMININ
Murdiya ce kawai na tarihin da Turawa waɗanda su ka kashe kusan dukkan dakarun Daular Sakkwato a 1903 cewa wai an yi Jihadin Fulani kuma wai an kwace ƙasar Hausa! Fassarar Kalmar CONƙUERED ko DEFEATED HAUSA KINGDOMS daga marubuta tarihin Yammawa ta fito amma ba daga Musulmi a Arewacin Nijeriya ba. Kai Shehu ma ba mulki irin na SULTANAWA ya yi ba amma ya tsaya kan muƙamin AMIR wato jagora na al’ummar Musulmi da su ka hada da kowace ƙabila. Masu amfani da rigar ƙabila don jirkita tarihin da gangan ko da ganganci su ke alaƙanta ƙabila a tajdidin don duk Musulmi sun sa hannu sun kawo gyara don amfaninsu da jikokinsu ba don ribar AMIRAL MUMININ ba.
Kamar yadda na yi bayani a rubutuna na baya, Shehu a iya ƙasar Gobir ya yi rayuwarsa har ya koma ga Allah bai taɓa zuwa inda yau ya ke Katsina, Kano, Zazzau da sauransu ba. Mutane masoya Musulunci kan tashi daga garinsu su taɓo wajen Shehu ya yi mu su addu’a sai su koma ƙasarsu don bunƙasa Musulunci ba don kafa sarauta irin ta gargajiya kamar yadda Bature ya canja tsarin zuwa yadda ya ke gudana a zamanin yau ba. Kun ga a yau ai gwamna ma kan iya ƙirƙirar masarauta ya nada wanda ya kwanta ma sa a rai, ba duba wani gado ko wai kwace garin wani ko wasu ba. Illa iyaka duk kasa na ƙarƙashin gwamnatin Bature ko tanadin tsarin mulki.
Don a gane batun ƙarara tajdidin Shehu bai kwace kowane gari ba amma mutanen garuruwan ke zuwa su karbi tuta don kawo canji a garuruwansu bisa bin addini sau da kafa, ba gwagwarmayar faɗaɗa gari ko masarauta ko girman gonaki da taskokin dukiya ba. Don haka duk wanda ya ce Shehu ya kwace wani gari zai yi bayani a gobe kiyama gaban Allah kuma kowane addini ya ke bi Allah zai yi ma sa hukunci.
Kafin tajdidin Shehu ba wata kasa dunƙulalliya ta Hausa sai dai garuruwan Hausa wato HAUSA STATES kuma a kan samu wannan Sarkin na takalar makwabcinsa don faɗaɗa ƙasa. Gaskiyar magana akwai waɗanda su ka dauka Shehu ya taho daga ƙasashen ƙetare ne ya na kora shahu da sauran ‘yan uwansa kawai su ka sauka a Gobir daga nan su ka ƙaddamar da jihadi! akwai ƙungurmin jahilci da a ka dade a na mannawa koyarwar Shehu a Arewa daga makircin Yammawa wadanda su ma su ka tallata addininsu ga Arewawa.
Masu cewa Shehu Mujaddadi ya kashe mu su iyaye, shin wa ya haife su tun da ba iyayensu fiye da shekaru 200? mu leƙa zazzau inda gidajen sarauta 3 na Mallawa, Katsinawa da Barebari ke sarauta
Masu kulla wannan makirci na murde tarihin koyarwar Shehu Danfodio na yin caraf su yi iƙirarin wai Shehu ya kashe mu su iyaye! Shin za a iya haifar mutum alhali an kashe iyayensa fiye da shekaru 200 da su ka wuce? Shin ko daga lahira iyayen su ka haifi mutanen nan masu iƙirari? Gaskiyar magana wa in ma dama karya su ke yi ba wanda ya kashe mu su ko kaza a danginsu ko kuma ba su da alaƙa ta kusa ko ta nesa da mutanen da su ke cewa an kashe.
Mu ma fara da iya arangamar da Shehu ya yi ta kare kansa daga yunƙurin kisan gilla na Sarkin Gobir Yunfa. Yunfa ya yi sanadiyyar kisa ga almajiran Shehu da dama kuma inda a 1808 almajiran Shehu su ka yi nasara kan Yunfa. Shin Sarki Yunfa shi ne uban dukkan Gobirawa? Amsa a nan a’a amma Sarki ne da ya yi sarautar Gobir daga 1801-1808 kuma ya ma fi kusa da Shehu daga masu amfani da sunansa a yau don kwangila tun da almajirin Shehu ne amma ya bijire don rashin kaunar haɓakar koyarwar Shehu.
Kama daga Sarkin Katsina a zamanin tajdidi wato Ummarun Dallaje zuwa kan Sarki Kano Mallam Sulaimanu duk ‘yan asalin yankunan da zuriyarsu ta ke ne har zuwa wannan zamanin. Na shaida mu ku Malam Ummarun Dallaje asalin iyayensa Larabawa ne na Wadai daga Chadi amma shi an haife shi a Dallaje da ke Katsina. Ba wani Bakatsine na kwarai da ke hamayya da gidan Malam Ummarun Dallaje.
KAMMALAWA
Ko a Kano da wasu ke sukar tajdidi da a ka naɗa Malam Sulaimanu, ba wani tsantsar Bakano da ke hamayya da wannan tarihi kuma hatta Kutumbawa da a ke magana ba su aiki kowa ya kai farmaki kan fadar Dabo ya kwace sarauta ba. Idan kuma akwai wanda a ka aika sai ya fito ya nuna shaidar hakan. Malam Sulaimanu Bakano ne daga zuriyar Mundubawa kuma malami ne mai son bunƙasa karatarwar Islama.
Ko Zazzau da a ke magana da Malam Musa ya zo da tuta ya kafa gidan Mallawa bai jagoranci kashe kowa ba don ma ai zuriyar Sarki Makau da a ka tarar ta kafa sabuwar hamshakiyar masarauta ta Suleja, kuma ba wani Bazazzagi na gaskiya da ke korafin Shehu ya kashe ma sa iyaye. Ashe masu wannan ikirari ‘yan kwangila ne ba su da alaka da masarautun nan ko zama dangin dakarun da su ka yi aiki da sarakunan da a ke magana. Zazzau ma a yau na da gidajen sarauta 3 na Mallawa, Katsinawa da Barebari, to me ya kawo batun kabila ko ƙabilanci?.
Duk Zallawa su nemi iyayensu can a kauyukansu amma tarihin nan bai nuna dangantakarsu ba ko miskala-zarratin.
