Kaduna: Adadin waɗanda suka rasu ya kai 30 yayin da ‘yan bindiga suka farmaki ƙauye

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kimanin mutane 30 ciki har da yara takwas, aka halaka bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari a ƙauyen Naridon da ke Gundumar Kamaru a Ƙaramar Hukumar Kauru ta Jihar Kaduna.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun afka wa ƙauyen ne da misalin ƙarfe 11:00 na daren Lahadi wayewar Litinin, inda suka riƙa harbe-harbe ba tare da ƙauƙautawa ba, lamarin da ya haddasa asarar rayuka da dama.

Haka kuma, maharan sun cinna wa gidaje da dama wuta, wanda hakan ya jefa mazauna ƙauyen cikin firgici tare da tilasta wa wasu tserewa domin tsira da rayukansu.

Sakataren dagacin ƙauyen mai suna Dogon Rana, ya tabbatar da faruwar al’amarin a wata hirar wayar tarho a ranar Litinin, inda ya bayyana harin am a matsayin ɗaya daga cikin munanan hare-hare da ƙauyen ya fuskanta a ‘yan kwanakin nan.

A cewarsa, an tabbatar da mutuwar mutane 30, amma ana fargabar adadin ya kere haka saboda akwai waɗanda suke ciki mawuyacin hali sakamakon raunuka da suka samu.

Har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoto, jami’an tsaro ba su fitar da cikakken bayani kan harin ba, yayin da ake cigaba da tattara bayanai akan adadin waɗanda suka jikkata da kuma irin ɓarnar da harin ya haddasa.

By Babaji