Talauci da shugabanci a Nijeriya

Spread the love

Daga SHEHU MUSTAPHA CHAJI

Rahoton bankin duniya na shekarar 2026 ya nuna cewa kimanin mutane miliyan 123 ne ke barazanar faɗawa cikin matsanancin talauci a Najeriya.

Haka kuma, rahoton hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) da aka fitar kwanan nan ya nuna cewa Jihar Sokoto ce ta fi kowace jiha fama da talauci a Najeriya. Jihohin da ke biye da ita sune: Taraba, Jigawa, Ebonyi, Adamawa, Zamfara, Yobe, Kebbi, Gombe, da Bauchi.

Abin lura a nan shi ne, cikin jihohi 10 da suka fi fuskantar barazanar talauci, in banda Jihar Ebonyi, dukkan sauran tara daga Arewacin Nijeriya suke.

To, tambayar anan ita ce: Shin riƙe shugabancin Najeriya na da alaƙa da rage ko kawo ƙarshen talauci?

Jihar Sokoto da a yanzu ta fi kowace jiha talauci — ɗan jihar daga tsohuwar Jihar Sokoto (Sokoto, Zamfara da Kebbi) ya mulki Najeriya. Haka kuma ɗan Jihar Adamawa ya riƙe muƙamin mataimakin shugaban ƙasa na tsawon shekaru takwas. Sannan nan kusa, ɗan Arewa daga Jihar Katsina ya mulki Najeriya na tsawon shekaru takwas (2015-2023).

Shin me ya sa suka gaza wajen magance talauci a Arewacin Najeriya?
Laifin al’umma ne ko na shugabanni?

Masu da’awar cewa matsalolin da ake fama da su a yanzu saboda ɗan Kudu ne ke mulki ba su da hujja!

Idan har zancensu gaskiya ne, to su kawo mana hujjojin da ke nuna raguwar talauci ko ƙaruwar wadata da arziki a Arewacin Najeriya daga shekarar 2015 zuwa 2023.

Duk mai bin diddigin bunƙasar tattalin arziƙi a Najeriya zai jinjinawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan kafa tubali da harsashin da zai ɗora Najeriya a tafarkin bunƙasar tattalin arziƙi, wanda masana ke hasashen nan da wasu shekaru Najeriya za ta zama ƙasa ta biyar a ƙarfin arziƙi a Duniya.

Kowa ya san yadda Shugaba Tinubu ya bunƙasa tattalin arziƙin Jihar Legas. Shi kuma jagoran ‘yan adawa, duk da damar da ya samu a Najeriya, Jiharsa ta Adamawa na cikin jerin jihohin da suka fi fuskantar barazanar talauci a Najeriya!

Mu haɗu mu kori talauci daga Najeriya ta hanyar sake zaɓen Shugaba Tinubu a wa’adi na biyu, domin samun damar kammala ayyukan ci gaba da manufofin da za su kai Najeriya ga ci gaba da arziƙi da wadata.

Shehu Mustapha Chaji
ya rubuto daga Kano

By ukarofi

Leave a Reply