Tarihin Muhammadu Kanta, wanda ya assasa Daular Kabi (II)

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Bayan da Muhammadu Kanta ya samu nasarar tabbatar da ‘yancin Daular Kabi, ya mayar da hankali wajen faɗaɗa mulkinsa. A cewar masana tarihi, mulkinsa ya bazu zuwa manyan yankuna na ƙasar Hausa da wasu sassan Yammacin Afirka.

A gabas, iyakar mulkinsa ta kai har yankin Nguru, a masarautar Borno ta tsohon lokaci. A yamma kuma ya miƙa ikonsa zuwa yankunan da suka yi iyaka da tsohuwar Daular Oyo. A arewa kuwa, ya mamaye yankunan Arewa, Zabarma da wasu sassan da yanzu suke cikin Jamhuriyar Nijar. Haka kuma ya shimfiɗa ikonsa zuwa wasu yankunan da yanzu suke cikin ƙasashen Burkina Faso da Jamhuriyar Benin.

Ginin Birnin Surame:

Bayan samun kwanciyar hankali, Muhammadu Kanta ya gina katafaren birnin Surame, wanda ya zama babban birnin Daular Kabi.

An kewaye birnin da ganuwa mai ƙarfi, tare da ƙofofi takwas da ake amfani da su wajen shiga da fita. Daga cikin ƙofofin akwai:

ƙofar Sarki, ƙofar Yaƙi, ƙofar Dashi, ƙofar Abaye, ƙofar Magaji, ƙofar Magajiya, ƙofar Abamu, ƙofar Zaure.

Baya ga waɗannan, akwai wata ƙaramar ƙofa da ake amfani da ita a lokutan gaggawa ko fita cikin sirri.

Har zuwa yau, ragowar ganuwar Surame na nan a ƙaramar Hukumar Silame da ke Jihar Sokoto, kuma wurin na daga cikin muhimman wuraren tarihi da ake ziyarta.

Tsarin mulki:

Muhammadu Kanta ya kafa ingantaccen tsarin gudanar da mulki, inda ya naɗa manyan masu riƙe da sarautu domin su taimaka masa.

Daga cikin sarautun da ya kafa akwai:

Magaji, Inname, Kokani, Magajin Baberi, Magajin Kulalu, Magajin Leka.

Yawancin waɗannan sarautu har yanzu suna cikin tsarin Masarautar Kabi.

Hare-haren Askiya Toure:

Bayan kafuwar Daular Kabi, Askiya Toure bai daina ƙoƙarin dawo da yankin ƙarƙashin mulkinsa ba.

Ya jagoranci hare-hare da dama kan Surame, amma rundunar Muhammadu Kanta ta ci gaba da fatattakar mayaƙansa.

Riwayoyi sun nuna cewa hari mafi muni shi ne wanda Askiya Toure ya jagoranta da kansa a kusan shekarar 1530. A wannan yaƙi ne rundunar Songhai ta yi asarar mayaƙa da dama fiye da yadda ta taɓa yi a baya.

Wannan yaƙi ya ƙara tabbatar da ƙarfin Daular Kabi da kuma bajintar Muhammadu Kanta a matsayin jagoran yaƙi.

Gadon tarihi:

Har yanzu akwai abubuwa da dama da suka rage daga zamanin Muhammadu Kanta.

Daga cikinsu akwai:

Ragowar ganuwar Birnin Surame.

Rijiyoyin da aka haƙa a lokacin mulkinsa.

Kayan amfanin gida irin su tukwane da shantali.

Takobin da ake cewa ya yi yaƙi da shi, wanda yanzu yake hannun Sarkin Kabi, Alhaji Sama’ila Muhammadu Mera, CON.

Wasu kayan kiɗa da aka ƙwato daga Daular Nupe bayan yaƙe-yaƙe.

Waɗannan kayan tarihi na jan hankalin masu bincike da baƙi daga sassa daban-daban na duniya.

Rasuwarsa:

Riwayoyi sun nuna cewa Muhammadu Kanta ya rasu a shekarar 1561 a garin Jirwa, kusa da Rinin ɗan Ashirta a yankin Katsina.

Daga bisani, aka ɗauko gawarsa zuwa Surame, inda aka binne shi.

Magajansa:

Muhammadu Kanta ya haifi ‘ya’ya huɗu:

Ahmadu, Ibrahim, Muhammadu, Kanna.

Bayan rasuwarsa, ɗansa Ahmadu, wanda kuma jikan Sarkin Arewan Matankari Bagaji ne, ya gaje shi a matsayin Sarkin Kabi.

Tun daga lokacin ne zuriyar Muhammadu Kanta ta ci gaba da riƙe sarautar Kabi har zuwa yau.

Jerin Sarakunan Kabi:

Masana tarihi sun lissafa jerin sarakunan Kabi tun daga Muhammadu Kanta kamar haka:

1. Muhammadu Kanta (1516–1561), 2. Ahmadu I (1561–1596), 3. Dawuda (1596–1619), 4. Ibrahim I (1619–1621), 5. Suleimana I (1621–1636), 6. Muhammadu (1636–1649), 7. Maliki ɗan Ibrahim (1649–1662), 8. Umaru Giwa (1662–1674), 9. Muhammadu Kaye (1674–1676), 10. Ibrahim II (1676–1684), 11. Muhammadu na Sifawa (1684–1686), 12. Ahmadu ɗan Amaru (1686–1696), 13. Tomo (1696–1700), 14. Muhammadu Can Giwa (1700–1717), 15. Samaila I (1717–1750), 16. Muhammadu ɗan Tagandu (1750–1754), 17. Abdullahi Toga (1754–1775), 18. Suleimana II (1775–1803), 19. Abubakar Ukar (1803), 20. Muhammadu Hodi (1803–1826), 21. Samaila II (1826–1827), 22. Samaila Karari (1827–1831), 23. Yakubu Nabame (1831–1854), 24. Yusufu Mainasara (1854–1859), 25. Muhammadu Ba’are (1859–1860), 26. Abdullahi Toga (1860–1883), 27. Samaila Sama (1883–1915), 28. Suleimana III (1915–1920), 29. Muhammadu Sama (1920–1934), 30. Muhammadu Sani (1934–1942), 31. Samaila III (1942–1953), 32. Muhammadu Shehe (1953–1959), 33. Muhammadu Mera, CON (1959–1996), 34. Alhaji Sama’ila Muhammadu Mera, CON (1996 zuwa yanzu).

Kammalawa

Muhammadu Kanta ya kasance ɗaya daga cikin fitattun jagororin ƙasar Hausa da suka kafa daula mai cin gashin kanta tare da kare ta daga manyan hare-haren Daular Songhai. Jarumtarsa, dabarun yaƙi da tsarin mulkinsa sun ba Daular Kabi damar bunƙasa tsawon ƙarni da dama.

Har yanzu, Surame, kayan tarihinsa da kuma zuriyarsa da ke ci gaba da mulkin Masarautar Kabi suna zama shaidar irin gagarumar gudunmawar da ya bayar ga tarihin Arewacin Nijeriya da ma Yammacin Afirka.

By ukarofi

Leave a Reply