Daga JOHN D. WADA a Lafiya
Shugaban ƙungiyar masu babur na ƙasa reshen jihar Nasarawa Kwamarade Yahaya Jibrin yace ƙungiyar ta daɗe tana bada gagaruman gudumawa a fannin tallafa wa ƙoƙarin gwamnatin jihar don samar da aikin yi da rage zaman banza tsakanin ɗimbin matasan jihar dama ƙasa baki ɗaya zuwa yanzu.
Kwamarade Yahaya Jibrin ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a ofishin sa dake tsohon gareji dake Lafia babban birnin jihar a makon da ake ciki.
Yace kawo yanzu mambobin ƙungiyar sun kai sama da mutum 3000 wato a garin Lafia kaɗai kenan banda sauran ƙananan hukumomi da ƙauyuka a jihar da sauran su haɗe da waɗanda suka fito daga wasu jihohin kuma galibinsu suna da iyalai kuma sun dogara ne ga wannan sana’ar ta acaba.
Baya ga wannan a cewar shugaban ƙungiyar tana kuma da karfin ƙuri’a na zaɓe inda mambobin sukan kuma fito kwansu da kwarkwata a lokutan zaɓe suna kaɗa ƙuri’a.
Haka kuma a cewar kKwamarade Yahaya Jibrin ƙungiyar kan horar da mambobinsu akai-akai don wayar da kawunansu game da dokokin aikin nasu tare da tallafa musu dai dai gwargwado a duk lokaci da buƙatar hakan ta taso.
Dangane da ƙwace babura da hallaka mambobinsu da wasu miyagun mutane keyi a birnin Lafia da wasu garuruwan Kwamared Yahaya yace ƙungiyar tana ƙoƙarin don magance lamarin musamman ta wayar musu da kai game da ire-iren fasinja da zasu riƙa ɗauka musamman da daddare da sauransu.
Kwamarade Yahaya Jibrin ya kuma yi amfani da damar inda ya yaba wa gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule dangane da tallafi da yake basu da kuma ayyukan cigaba da yake gudanar a jihar musamman sabbin hanyoyi da gadoji irin na zamani musamman wanda ke Lafia a yanzu da ya gina dake cigaba da rage junkuso wa mutanensa da sauran masu abubuwan hawa baki ɗaya a jihar sai dai ya kuma yi roƙon gwamnati ta samar wa mambobinsu da asibitoti da sauran abubuwan more rayuwa don a cewarsa ƙungiyar na taimaka matuƙa wajen samar wa gwamnatin kuɗaɗen shiga ta haraji da mambobin nasu ke biya kullum.
Daga karshe sai shugaban ƙungiyar na masu babura a jihar kwamred Yahaya Jibrin ya kuma yaba wa kyakkyawar haɗin kai da dangantaka dake tsakanin ƙungiyar da sauran ƙungiyoyin sufuri a jihar inda ya buƙaci a cigaba da wannan haɗin kai don cigaban fannin baki ɗaya.
