
Attajirin Nijeriya kuma shugaban rukunin kamfanonin Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote na shirin sadaukar da wani kaso mai yawa na dukiyarsa domin tallafa wa ayyukan jin ƙai, inda ɗiyarsa Halima Ɗangote, ta bayyana cewa mahaifin nata na da niyyar ware kashi ɗaya bisa uku na dukiyarsa domin taimakon jama’a.
Halima ta bayyana cewa, wannan shiri wani ɓangare ne na burin mahaifinta na amfani da dukiyarsa wajen samar da sauƙi da inganta rayuwar al’umma, musamman ta fannonin lafiya, ilimi da rage ƙalubalen talauci.
Dangote, wanda ke cikin jerin attajiran da suka fi kowa arziki a duniya, na da dukiyar da aka kiyasta ta kai kusan dala biliyan 35.1. Idan aka aiwatar da wannan shiri, zai kasance ɗaya daga cikin manyan gudummawar da wani attajiri daga Afirka ya bayar wajen ayyukan agaji.
A tsawon shekaru, Aliko Dangote ya kasance mai gudanar da ayyukan tallafi ta hannun gidauniyarsa, inda aka mayar da hankali kan fannoni kamar samar da abinci, tallafin lafiya, taimakon marasa galihu da ayyukan ci gaban al’umma.
Masu bibiyar harkokin jin ƙai na ganin irin wannan mataki daga manyan ‘yan kasuwa na iya taka muhimmiyar rawa wajen rage wasu matsalolin da al’umma ke fuskanta tare da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin masu hannu da shuni da jama’a.
Sai dai har yanzu ba a bayyana cikakken bayani kan lokacin da za a fara aiwatar da shirin ko yadda za a raba wannan kaso na dukiyar ba.
Me kuke ganin irin wannan mataki zai iya haifarwa ga ci gaban al’umma? Shin ya kamata manyan attajirai su ƙara mayar da wani kaso na dukiyarsu wajen ayyukan jin ƙai? Ku bayyana ra’ayoyinku a sharhi.
