
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Tinubu ya umarci rundunonin soji da ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro da su gaggauta ƙaddamar da atisayen farauto waɗanda suke da hannu a mummunan harin da aka kai wa al’ummar ƙauyen Naridon da ke Gundumar Kamaru a Ƙaramar Hukumar Kaurun Jihar Kaduna.
Kakakinsa Bayo Onanuga ne ya sanar da haka a wata takarda, ranar Talata.
“In mai umartar sojoji, ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro da su ƙaddamar da atisaye a yankunan da abin ya shafa domin kama waɗanda suke da hannu da kuma dawo da doka da oda a shiyyar,” inji Tinubu.
Haka kuma, shugaban ya jaddada aniyar gwamnatinsa ta ƙarfafa fanin tsaro a ƙasar da kuma lalata dukkan hanyoyin aikata ta’addanci da ke barazana ga zaman lafiya da ɗorewar al’amura.
Shugaban ƙasar ya kuma kirayi ‘yan Nijeriya da su cigaba da ba wa hukumomin tsaro agaji wajen ba su muhimman bayanan tsaro akan lokaci domin ɗaukar matakan da suka dace.
Umarnin shugaban na zuwa ne bayan harin ƙauyen Naridon a safiyar ranar Litinin, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar kusan mutane 30 ciki har da mata da yara da kuma lalata gidaje da dama.
