
Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta soke hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ya umarci Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta soke rajistar jam’iyyar adawa ta ADC da wasu jam’iyyu huɗu bisa rashin cika wasu sharuɗɗan shiga zaɓe.
Kotun, a hukuncin da alƙalai uku suka yanke, ta ce babbar kotun ba ta da hurumin sauraron shari’ar, saboda ƙarar da aka shigar ba ta cika ka’idojin doka ba.
Haka kuma, ta bayyana cewa babu ingantacciyar ƙara da za ta bayar da damar umarnin cire rajistar jam’iyyun a dokance.
Kotun ta ce alkalin babbar kotun ya yi watsi da hujjojin da suka nuna cewa jam’iyyun sun taɓa lashe kujeru a zaɓukan baya, tare da yin hukunci duk da umarnin dakatar da ci gaba da sauraron shari’ar da kotun ɗaukaka ƙara ta bayar.
Saboda haka, Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tabbatar da cewa jam’iyyun da abin ya shafa har yanzu suna da cikakkiyar rajista. Jam’iyyun sun haɗa da ADC, Action Peoples Party (APP), Action Alliance (AA), Accord Party (AP) da Zenith Labour Party (ZLP).
Da fari, Babbar Kotun Tarayya ta umarci INEC ta soke rajistar jam’iyyun biyar, tare da hana su shiga harkokin zaɓen 2027, bayan ƙungiyar National Forum of Former Legislators (NFFL) ta yi zargin cewa sun gaza cika sharuddan kundin tsarin mulki na ci gaba da kasancewa a matsayin jam’iyyun siyasa. Sai dai dukkan jam’iyyun da INEC sun ɗaukaka ƙara, lamarin da ya kai ga soke hukuncin.
