Gwamnatin Abdullahi Sule ta cire wa ‘yan fansho kitse a wuta – Hudu Baba Abdullahi

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafia

Shugaban ƙungiyar ‘yan fansho na jihar Nasarawa Hudu Baba Abdullahi yace gwamnatin jihar ta Injiniya Abdullahi Sule zuwa yanzu za a iya cewa ta cire wa masu karɓan fansho na jihar kitse a wuta idan aka yi la’akari da makudan kuɗaɗe da gwamnan ke cigaba da amincewa don warware matsalolin ‘yan fansho din a jihar baki ɗaya.

Ya bayyana haka ne a lokacin da yake amsa wasu tambayoyi daga ‘yan jarida da suka ziyarci ofishin ƙungiyar ta ‘yan fansho dake garin Lafia fadar gwamnatin jihar ranar Talata na makon nan.

Hudu Baba Abdullahi yace kafin zuwan Gwamna Abdullahi Sule kan mulki ‘yan fansho a jihar sukan karɓi rabin kuɗin fanshon ɗinsu ne na wata-wata amma zuwan gwmnan ke da wuya sai ya umurci hukumar dake kula da harkokin ‘yan fanshon ɗin ta gaggauta dakatar da tsarin na rabin albashin ta soma biyansu cikakken haƙƙinsu ba tare da ɓata lokaci ba.
Yace daga wannan lokaci zuwa yanzu gwamnatin jihar ta Abdullahi Sule aƙalla ta kashe kuɗi sama da biliyan 50 ne don biya wa ‘yan fanshon hakƙinsu waɗanda a cewarsa galibin kuɗaɗen suna bin gwamnatocin jihar da suka shuɗe ne ba ta Abdullahi Sule din ba inda gwamnan ya kuma yi alƙawarin cigaba da hakan har ƙarshen wa’adin gwamnatinsa.

Shugaban ƙungiyar ta ‘yan fanshon jihar Nasarawa Hudu Baba Abdullahi ya kara da cewa akan haka nema yasa ƙungiyar ta yanke shawarar naɗa wa babban ofishin ƙungiyar dake Lafia sunan Gwamna Abdullahi Sule din don karrama shi da kuma nuna matuƙar godiyarsu ga gwamnan.
Dangane da wasu nasarori da ƙungiyar ta cimma zuwa yanzu ƙarƙashin jagorancinsa a matsayin shugaban ƙungiyar a jihar kimanin shekaru biyar kenan zuwa yanzu shugaban Hudu Baba Abdullahi ya bayyana cewa a ƙarƙashin shugabancinsa ƙungiyar ta tabbatar da biyan mambobinta ‘yan fashon ɗin cikakken albashinsu na fanshon ɗin inda ta kuma kafa wa mambobin nasu wata ƙungiyar adashi na musamman inda suke tara wasu kuɗaɗe lokaci-lokaci da hakan ke taimaka musu da gina tareda yi wa ginin babban sakatariyar nasu kwaskwarima da dai sauran su da dama inda a ƙarshe ya sake yin amfani da damar yayi kira na musamman ga gwamnatin na jihar ta ƙarasa biyan sauran basussuka da ‘yan ƙungiyar ke bin gwamnati waɗanda a cewarsa koda yake yawancin basussukan ba tana bin gwamnatin Abdullahi Sule na yanzu bane na da suka shuɗe ne.

By ukarofi

Leave a Reply