Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Shugaban kwamitin haɗin gwiwa na yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi na Jihar Kano, Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya bayyana cewa kusan kashi 70 cikin 100 na manyan laifukan da ake aikatawa a jihar suna da alaƙa da shan miyagun ƙwayoyi.
Muhuyi Magaji ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da manema labarai a Kano, inda ya buƙaci kafafen yaɗa labarai su mara wa gwamnatin jihar baya wajen wayar da kan al’umma kan illolin shan miyagun ƙwayoyi, fataucin haramtattun ƙwayoyi da kuma ayyukan ‘yan daba.
Ya ce, bisa ga ƙididdigar rundunar ‘yan sandan Jihar Kano, an kama mutane kimanin 3,080 da ake zargi da aikata manyan laifuka a faɗin jihar a shekarar da ta gabata, inda kusan kashi 70.2 cikin 100 na laifukan ke da alaƙa da shan miyagun ƙwayoyi.
Ya ƙara da cewa, da an samu nasarar shawo kan matsalar shan miyagun ƙwayoyi tun da wuri, da ba a samu dubban waɗannan laifuka ba. Saboda haka ne gwamnati ta ƙuduri aniyar magance matsalar ta hanyar wannan kwamitin haɗin gwiwa.
Kazalika, Muhuyi Magaji ya bayyana cewa, an kafa kwamitin ne bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ayyana shan miyagun ƙwayoyi a matsayin matsalar gaggawa ta lafiyar al’umma a jihar, tare da ba shi alhakin yaƙi da fataucin haramtattun ƙwayoyi, gyaran halayen masu shaye-shaye da kuma gurfanar da masu laifi a gaban kotu.
A cewarsa, dabarun kwamitin ba su taƙaitu ga kama masu laifi kawai ba, har ma sun haɗa da hana yawaitar matsalar, gyaran halayen waɗanda suka kamu da shaye-shaye da kuma haɗa kan al’umma domin magance matsalar baki ɗaya.
Ya ce kwamitin zai yi aiki tare da al’ummomi, hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki domin gano tushen matsalar shan miyagun ƙwayoyi da kuma daƙile laifukan da ke da alaƙa da ita.
Shugaban kwamitin ya kuma yi gargaɗi ga ƙungiyoyin masu tayar da tarzoma da ke da alaƙa da shan miyagun ƙwayoyi, yana mai cewa gwamnatin jihar za ta yi amfani da tanade-tanaden doka wajen hukunta duk wanda aka samu yana aikata abin da zai iya kawo cikas ga zaman lafiya da tsaron al’umma.
Ya jaddada aniyar kwamitin na rage yawaitar shan miyagun ƙwayoyi da laifukan da suke haddasawa ta hanyar haɗin gwiwar hukumomin gwamnati, jami’an tsaro, shugabannin al’umma, kafafen yaɗa labarai da sauran masu ruwa da tsaki.
