
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Kimanin mutane bakwai ne aka halaka yayin da aka sace wasu da dama a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka afka wa ƙauyen Tsamaye da ke Ƙaramar Hukumar Sabon Birni a Jihar Sakkwato.
An ruwaito cewa, uku daga cikin waɗanda suka rasu an kashe su ne a masallaci yayin harin, wanda aka ƙaddamar da misalin ƙarfe 8:30 na daren Talata wayewar Laraba kuma ya ɗauki tsawon sa’o’i bakwai ba tare da tsayawa.
Mazauna yankin sun ce, maharan sun kutsa yankin ne cikin adadi mai yawa, inda suka riƙa harbe-harbe tare da farmakar mutane a gidajensu, sace kayayyaki a shaguna da sace dabbobi.
Wani shaida da ya zanta da jaridar Daily Trust ya ce an gano gawarwakin mamatan ne a washe-gari bayan maharan sun bar yankin.
A cewarsa, ‘yan bindigar sun yi wa jami’an tsaron da aka jibge a yankin ne ba-zata, sakamakon zagaye ƙauyen da suka yi da hana su mayar da martani a lokacin da suka samu kiran gaggawa daga ‘yan yankin.
Ya bayyana cewa, jami’an tsaron na iya bakin ƙoƙarinsu wajen ba su kariya tare da taimaka wa wasu ƙauyuka da ke ƙaramar hukumar.
Ya ƙara da cewa, biyu daga cikin waɗanda aka halaka ‘yan asalin ƙauyen ne, yayin da biyar ɗin kuma sun kasance cikin masu gudun hijira a garin.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Sakkwato, DSP Ahmad Rufa’i ya tabbatar da cewa an sanar da su kan al’amarin kuma ƙoƙarin fitar da ƙarin bayani a kai da zarar sun kammala bincike.
