Gwamnatin ƙasar Malta tana gayyatar ‘yan Nijeriya da su zo su yi mata aiki

Spread the love

Daga AMINA YUSUF ALI

Gwamnatin ƙasar Malta da ke cikin nahiyar Turai ta ƙudiri niyyar ba da guraben aiki ga ƙwararrun ‘yan wasu ƙasashen da ke wajen nahiyar ta Turai kamar dai ‘yan Nijeriya. Inda suka sauƙaƙa hanyar neman ga masu neman aiki da ba ‘yan ƙasar ta Malta ba.

Wannan yunƙuri wani martani ne da ƙasar ta yi wanda ya biyo bayan kira da nuni da Ƙungiyar Tarayyar Turai ta yi ga ƙasar a kan ta yi wani abu a game da matsalar ƙarancin ma’aikatanta.

Tun a Janairun shekarar bana ne dai gwamnatin ƙasar Malta ta ƙirƙiro da wannan shiri na taimakon ma’aikata daga ƙasashen duniya wajen samun aikin yi mai tsoka a ƙasar.

Rahotanni sun bayyana cewa kowa yana iya neman aikin kama daga masu digiri da sauran ƙwararru a kan albashi na aƙalla Yuro 25,000 duk shekara. Wani zubin ma har zuwa 35,000.

Malta tana daga cikin ƙasashen Turai da suke kan tsarin yankin Schengen. Wato ƙasashen da suka yi watsi da tsananta fasfo don shigar su, da kuma ƙyamar masu hijira. Ko a bodarsu ba a buƙatar ka kawo fasfo kafin ka ƙetara.

Kodayake, za a buƙace su da su kawo wasu takardun su nuna ga jami’an shige da ficen da suke a bodar ƙasar.

Sai dai kuma ƙasar za ta ba wa ‘yan Nijeriya wannan damar ne idan suna da muhalli kuma sun samu izinin zama a ƙasar ta Malta.

Ƙasar ta Malta dai a halin yanzu ta wallafa matakan da za a bi don samun gurbin aiki da samun damar zama a ƙasar a shafinta na yanar gizo.

By Editor