Gwamnatin Tarayya ta janye tuhumar cin amanar ƙasa da ta ke yi wa Sowore

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayya ta janye tuhumar da ta ke yi wa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC kuma mawallafin jaridar Sahara Reporters, Omoyole Sowore.

Gwamnatin Tarayyar ta janye tuhumar ce da ta ke yi na zargin cin amanar ƙasa a kansa a ranar Laraba 14 ga watan Faburairu.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Babbar Kotun Tarayya ta fitar a ranar Laraba 14 ga watan Faburairu.

Antoni Janar na Gwamnatin Tarayya, Lateef Fagbemi shi ya miƙa takardar dakatar da tuhumar kan mamallakin gidan jaridar Sahara Reporters.

Sanarwar ta ce, “Duba da sashi na 174(1) na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999 wanda aka yi wa gyaran fuska.

“Ganin ikon da wannan sashi ya bani, ni Lateef Olasunkanmi Fagbemi, SAN na janye wannan tuhuma mai ɗauke da lamba FHC/ABJ/CR/235/2019.”

Sowore wanda ya yi takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar AAC ya kasance mai yawan kushewa da kuma zagin gwamnatin Bola Tinubu kan tsarte-tsarenta.

An gurfanar da Sowore da Bakare a gaban babbar kotun tarayya Abuja a shekarar 2019, biyo bayan wata zanga-zangar da ya gudanar a Abuja mai taken “A Yi Juyin Mulkin Yanzu.”

A baya dai mai shari’a Emeka Nwite na babbar kotun tarayya da ke Abuja, ya yi barazanar yin watsi da tuhumar da ake masa na cin amanar ƙasa idan gwamnatin Nijeriya ba ta shirya cigaba da shari’ar ba bayan shekaru biyar.

Alƙalin ya yi gargaɗin ne a ranar Laraba a cigaba da sauraron ƙarar.

Shari’ar da aka shirya gudanarwa ba za ta ci gaba ba, kasancewar wanda ake tuhuma na 1 ya kasa amsa roqonsa biyo bayan sanarwar da sabuwar lauyan mai gabatar da ƙara ta yi, inda ta ce za ta ɗauki nauyin shari’ar ne bisa dalilin da lauyan da ke kula da shari’ar ya yi tun farko inda ala sauya sheƙa daga ma’aikatar shari’a.

Daga baya ta buƙaci a ɗage zamanta domin ta samu damar yin karatu da kuma sanin alnihin lamarin.

Lauyan da ake ƙara, Marshal Abubakar, ya ƙi amincewa da buƙatar ne saboda masu gabatar da ƙara na wasa al’amarin domin ɓata lokacin kotun.

By Editor