CBN ya dakatar da kamfanonin mai biyan kashi 100 a ƙasar waje

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya dakatar da kamfanonin mai na ƙasa da kasa mayar da kashi 100 na kuɗaɗen musaya na ƙasashen waje zuwa ga kamfanonin ƙasashen waje a lokaci guda.

Bankin ya ce, kamfanonin mai na ƙasa da ƙasa na iya mayar da kashi 50 na kuɗaɗen da suka samu a matakin farko sannan sauran rabin bayan kwanaki 90.

Daraktan sashen ciniki da musayar kuɗi na babban bankin, Hassan Mahmud ne ya bayyana haka a wata takardar da aka fitar mai ɗauke da kwanan wata 14 ga Fabrairu, 2024.

Babban bankin na CBN ya ce ya lura cewa ana fitar da kuɗaɗen ɗanyen mai da kamfanonin mai na Duniya (IOCs) da ke aiki a Nijeriya ke fitarwa zuwa ƙasashen waje don samun asusun iyayen IOCs a wani al’amari da aka kwatanta a matsayin ” haɗa kuɗi”.

“Wannan yana da tasiri kan hauhawar farashin kayayyaki a kasuwar canji na cikin gida,” in ji babban bankin.

“A bisa sauye-sauyen da ake yi a kasuwar canji, ya zama wajibi a ɗauki matakan shawo kan lamarin. Saboda haka, CBN ta bada umarni kamar haka;

“An ba wa bankuna damar tara tsabar kuɗi a madadin IOCs, bisa la’akari da matsakaicin kashi 50 na kuɗaɗen da aka dawo da su zuwa ƙasashen waje a matakin farko;

“Za a iya dawo da ma’auni 50 bayan kwanaki 90 daga ranar shigar da kuɗaɗen fitar da kayayyaki.”

By Editor