Ya kamata mu jinjinawa ƙoƙarin mata

Tare da ABBA ABUBAKAR YAKUBU

A wasu shekaru da suka gabata, tashar rediyon BBC ta taɓa gabatar da wata tambaya ta kacici-kacici mai taken, Wane ne yake da tasiri a rayuwarka? Masu sauraro daga sassan duniya daban-daban sun yi ta bayyana tunane-tunanensu, dangane da wanda suke ganin shi ne ya fi tasiri a rayuwarsu. Wani mai sauraro daga wata ƙasar Turai ya bayyana cewa, matarsa ce ta fi komai tasiri a rayuwarsa, sakamakon ita ce ke sarrafa duk wani abu da ya shafe shi.

A lokacin na daɗe ina jinjina wannan magana da mamaki a kanta, mai yiwuwa ƙila saboda yadda tunanin mu na ’yan Afrika da al’adunmu suka sha bamban ne. Ta yadda abu ne mawuyaci a nan Arewa a samu mutumin da zai fito gidan rediyo ya amsa da cewa matarsa ce take sarrafa rayuwarsa. Domin kuwa nan take za a fara samun wasu da za su laƙaba masa sunan ‘Mijin Hajiya.’

Al’adu da dokokin ƙasashen Turai sun bai wa mata matuƙar muhimmanci a rayuwar iyalinsu, saɓanin a nan Afrika inda maza ne mafiya tasiri da ƙarfin iko a cikin iyali. Kowanne daga ciki akwai dalilan da suka haifar da samuwar hakan a cikin ɗabi’ar zamantakewarsu, musamman ma dai yadda addini ya yi ƙarfi wajen tafiyar da rayuwar al’umma.

A nan Nijeriya, inda akasari maza ne suke ɗaukar nauyin tafiyar da hidindimun iyali da rayuwa, tasirin mata ya kasance mai rauni. Sai dai ta bayan fage, inda tasirinsu wajen tafiyar da harkokin cikin gidajen aurensu yake da muhimmanci sosai, wannan kuma ya sa hatta a rayuwar mazajensu na aure suke taka rawa ta musamman.

Maza ne aka sani da ɗaukar nauyin ciyarwa, biyan kuɗin haya, kuɗin makaranta, kula da lafiya, sutura, da sauran nauye-nauyen gida. Yayin da aka bar wa mata ɗawainiyar kula da gida, raino, tarbiyya, girki, kula da maigida da yara da sauransu. Kowa dai ya san matsayinsa da kuma nauyin iyali da ke kansa. Sai dai lokaci zuwa lokaci wani sashi ya kan riqa tallafawa wani sashi don samun sauƙin sauke nauyin da ke kansa.

Sannu a hankali wannan tsari na zamantakewa ya fara rushewa, saboda canjin zamani da taɓarɓarewar tattalin arzikin ƙasa. Maza da dama sun fara gazawa wajen sauke nauyin da ke kansu. Sakamakon tsadar rayuwa, da rashin kuɗaɗe a hannun jama’a. Maza da dama sun fara sarayar da wasu haƙƙoƙin iyali da ke kansu, saboda wahalhalun yau da kullum. Kasuwanci ba ya tafiya yadda ake buƙata, jarin ‘yan kasuwa da dama ya lalace.

Albashin ma’aikata ya yi ƙarancin da ba ya iya biyan ɗimbin buƙatu da nauye-nauyen iyali da ‘yan uwa masu sa rai da samun kulawa. Wannan ta sa wasu mata suka fara yunƙurin ganin sun taimaka wajen ɗaukar nauyin wasu abubuwa na gida ko na iyali. Kamar taimakawa wajen cefane, biyan kuɗin makarantar yara, kula da lafiya, har ma da biyan kuɗin haya idan ta kama.

Duk da kasancewar ba duka maza ne ke amincewa suna karɓar tallafi daga iyalinsu ba, saboda rashin yarda da kasawa ko gazawa wajen sauke nauyin iyali, da kuma gudun gori daga wajen wasu matan, musamman idan an samu saɓani. Amma ta tabbata cewa, hannu ɗaya ba ya tafi, kuma rayuwa ta yi matuƙar canzawa fiye da tunanin mutum. Don haka tafiyar da rayuwar iyali, a wannan yanayin, ba na mutum ɗaya ba ne.

Yadda mata da dama a gidajen mazajensu suka fahimci cewa, lallai iyalinsu na buƙatar gudunmawarsu, kuma suka duƙufa wajen ganin sun tallafa domin a rufawa kai asiri, a gudu tare a tsira tare, babban abin a yaba ne. Saɓanin yadda a baya sai dai a yi ta ɗora lissafi, ana bin maigida bashin kuɗin cefane, ko wata buƙata da aka zartar a gida lokacin ba ya nan, ko kuma bashi da kuɗi a lokacin. Amma a yanzu haɗa kai ake yi ana tattaunawa don gano ta ina za a taimakawa juna.

A saboda haka, wannan maƙala ta yau take kira ga sauran magidanta su riƙa nuna kulawa da yabawa ga ƙoƙarin da matansu ke yi na taimaka musu wajen sauke nauyin da ke kansu. An ce, durƙusawa wada ba gajiyawa ba ne. Kuma yaba kyauta tukuici. Yaba musu, da yi musu addu’ar sakayyar ubangiji, da zuga su domin ƙarfafa musu gwiwa, yana da tasiri sosai wajen tausasa musu zuciya. Babu shakka mata mutane ne masu tausayi da kuma rauni, suna buƙatar sanin ana jin daɗin abin da suke yi. Ana kuma yabawa ƙoƙarinsu, domin kada shaiɗanun ƙawaye da ’yan gaza-gani su samu shiga zuciyoyinsu.

Mata da dama sun rungumi kasuwanci da sana’o’i a gidajensu da ta hanyoyin sadarwar zamani, domin samarwa kansu wasu hanyoyin shigar kuɗaɗe da rufawa kai asiri. Ba tare da sun naxe hannu sun yi jiran gawon shanu ba. Saboda inda suke sa ran samu ɗin ba ya samuwa yadda suke so, ko a lokacin da suke buƙata. Gwamnati da ƙungiyoyin sa-kai da masu hannu da shuni suna ɗaukar nauyin koyawa mata ƙananan sana’o’i irinsu ɗinki, kwalliyar mata, haɗa man shafawa da man zafi, da ruwan sinadarin wankin kaya da na mota, haɗa turaren wuta, girke-girke, da kayan ƙwalama na soye-soye, duk domin su riƙa samun abin riƙewa a hannu, da kashe wutar gabansu.

Sakamakon dagewa da suka yi da neman na kai, ta hanyar rungumar ƙananan sana’o’in dogaro da kai, mata sun zama ’yan kasuwa sosai, wasu ma suna da manyan jari fiye da na mazajensu na aure. Wasu sun mallaki kadarori da manyan shagunan kasuwanci, ko abubuwan cinikayya, da suka ɗora wasu yardajjun mazaje a kai suna tafiyar musu da su.

A yayin da muke ƙarfafa gwiwar mata su kama sana’a, don su tallafawa iyali, kuma taimaki kansu, muna kuma jan hankalin maza su sani, yawon kasuwanci ba na mata ba ne, yanayin rayuwa ne ya kawo haka. Dole ne maza mu dage da sana’o’i iri-iri, don mu rufawa kanmu asiri, kuma mu tsare mutuncin matanmu. An ce sana’a goma maganin mai gasa, kuma babu maraya sai rago.

Kada ganin mata na taimakawa a gida mu naɗe hannu mu barsu da nauyin ciyar da kansu da iyalinmu waɗanda wajibinmu ne kula da buqatunsu. Mata taimako ne nasu, amma ba a ce mu zame kanmu mu barsu da ɗawainiya ba, mu kuma mu koma cin daɗi a waje, ko kashewa wasu matan waje, waɗanda ba wajibinsu ba. Alhalin na gida na can suna cin kwakwa, da fafutukar yadda za a rufawa kai asiri.

Wajibin mu ne mu tabbatar da ganin wannan halin da ake ciki ya sa mu cikin mutuwar zuciya da karaya ba. Mu ƙarfafa wa kanmu gwiwa, mu kuma cigaba da rarrashin matanmu ta hanyar gaya musu maganganu masu taushi da za su sanyaya musu zuciya, kuma mu nuna ƙoƙarin da muke yi a aikace, wajen rufa musu asiri da rage musu wahalhalun rayuwa. Mata suna buƙatar samun tabbacin kulawa, nuna ƙauna, da riƙon amana daga mazajensu na aure, ba lallai sai miji mai arziki ba, matuƙar mace za ta samu farinciki da kwanciyar hankali, talauci bai cika damunta ba.

Allah Ya ba mu zaman lafiya a tsakaninmu da iyalinmu, kuma Ya ba mu zuciyar haƙuri da juna. A daidai wannan lokaci da ake fuskantar yawaitar rabuwar aure, saboda tsadar rayuwa.