Ra’ayi

Matsayin wasan kwaikwayo (fim) a yau

Matsayin wasan kwaikwayo (fim) a yau

Daga MUHAMMAD UBALE ƘIRU Kafin na shiga cikin wannan maudu'i, ina so mai karatu ya fadada fahimtarsa a kan wannan batu, ya kuma yi hakurin karanta wannan rubutu har zuwa karshe kafin ya yi raddi ko fassara ga wannan maudu'i. Sannan yana da kyau mai karatu ya sani cewa, wannan ra'ayi ne da kuma fahimta irin tawa, kuma hakki ne na ilimi ka bai wa kowa damar tsayawa a kan wani ra'ayi ko furta fahimta. Da farko, makasudin wannan rubutu shi ne don karin haske ko fadada bayani a kan wani batu da Shaikh Malam Ibrahim Khalil ya fara tattaunawa…
Read More
Basaja a zaman aure (2)

Basaja a zaman aure (2)

Tare da AMINA YUSUF ALI Sannunku da jimirin karatun shafin Zamantakewa na jaridarku mai farin jini ta Manhaja! A wannan mako mun kawo muku yadda wasu ma'aurata suke yin basaja a zaman aure. Wanda abu ne da yake taka muhimmiyar rawa wajen kawo rikici a gidajen aure har ma idan abu ya yi qamari ya kai ga rusa auren gabadaya. A makon da ya gabata mun fara kwararo muku bayani ya zu kuma za mu dora a kashi na biyu na wannan maudu'in. A sha karatu lafiya. Haka su ma mata akwai kawaye da za su dinga cika muku baki…
Read More
Ashe ɓarayin mutane sun shigo Abuja?

Ashe ɓarayin mutane sun shigo Abuja?

Tare da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Da shigowa Abuja dan Nijeriya zai san ya shigo birnin da shugaban kasa ya ke da zama don ganin manyan ofisoshin jami'an tsaro kama daga na soja, 'yan sanda, jami'an tsaron farar hula da sauarn su. Ga mutane masu wutar jiniya na zirga-zirga. Barikoki kadai a bayan fadar shugaban kasa ta Aaso Rock na nuna akwai bambancin tsaro daga sauran yankunan kasa. Ba lalle ne birnin na da yawan dogayen gine-gine ba amma dai ga dogayen kamarorin tsaro a sassa daban-daban da ko su na aiki ko ba sa yi wannan sai jami'an tsaro ne…
Read More
Akwai buƙatar malamai su duba lamarin walimar sauka da ake yi yanzu

Akwai buƙatar malamai su duba lamarin walimar sauka da ake yi yanzu

Daga SALIHA ABUBAKAR ABDULLAHI, Zariya A zamanin dauri duk lokacin da iyaye suka ga 'ya'yansu sun kusa sauke Alkur'ani mai girma zuciyarsu kan cika da murna da farin ciki ne tare da fatan Ubangiji ya nuna musu lokacin. Idan ranar ta taho masu aka tabbatar da hakan, iyaye kan bi malamai da kyautar da ba ta taka kara ta karya ba don nuna godiya ga malaman da kara musu kwarin gwiwa domin su kara jajircewa kan abinda suke yi, su kuma su karva suna farin ciki da matukar godiyar karamcin da iyayen yara suka nuna musu. Idan makarantar allo ce,…
Read More
Fargabar matsalar tattalin arzikin Nijeriya

Fargabar matsalar tattalin arzikin Nijeriya

A makon da ya gabata, Bankin Duniya ya fitar da rahotonsa kan tabarberewar tattalin arzikin Nijeriya. Rahoto a karkashin duba irin cigaban da Nijeriya ta samu, Cibiyar Hada-hadar Kudi Ta Duniya ta bayyana cewa, tabarbarewar yanayin tattalin arzikin Nijeriya na kara jefa al'ummar kasar cikin wani hali. Rahoton ya nuna cewa, hauhawar farashin kayayyaki ya zama annoba ga rayuwar ’yan Nijeriya wanda dole ne hukumomi su yi yaki da hakan. Habakar hauhawar farashin kayayyaki da ke fitowa daga matsalar rashin tsaro, Bankin ya ce, zai iya jefa karin 'yan Nijeriya miliyan daya cikin matsanancin talauci. Tabbas tashe-tashen hankulan da hauhawar…
Read More
Fitar matasan Arewa ƙasashen waje: Ya kai mai shirin fecewa, ga wata ’yar shawara

Fitar matasan Arewa ƙasashen waje: Ya kai mai shirin fecewa, ga wata ’yar shawara

Daga MUHAMMAD SULAIMAN ABDULLAHI A mafi yawan lamura, za ka samu akwai alheri, kuma akan samu akasinsa. Don haka, a irin wannan dambarwar da mafi girman abin da ya jawo ta shi ne rashin kyakkyawan shugabanci, dole sai an yi taka-tsan-tsan. Lallai masu jan ragamar jagorancin al'umma a Najeriya, yawancinsu suna ha'intar al'umma.  Wani bawan Allah yake cewa da fita ko fecewa daga qasa abu ke mai sauki, to watakila shugabannin kasarmu sai dai su juyo su ga ba kowa, kowa ya kama gabansa. To shi dan'adam da Allah ya yi shi ba ya son a hana shi walwalar abin…
Read More
Tasirin fina-finan Hausa sun wuce yadda ake ɗaukar su a ƙasar Hausa

Tasirin fina-finan Hausa sun wuce yadda ake ɗaukar su a ƙasar Hausa

Daga ZAHRADDEEN IBRAHIM KALLAH Wato fina-finan Hausa sun yi nisa wajen jan hankalin al'umma. Ko shakka babu wannan dama ce da za a yi amfani da ita wajen sauya tunanin al'umma zuwa ingantatciyar rayuwa da bin dokoki.  Kwanakin baya a kafofin sada zumunci har majalusu na unguwanni, maganar da na ji ana ta yi ita ce wai raba gardama ya bayyana. Da yake na kwana biyu ba na kallo, na ce wanene wannan raba gardama? Ashe a cikin shirin Labarina ne na Malam Aminu Saira. A satin nan da muka fita daga shi, sai na ji sabon batu. Ko'ina maganar…
Read More
Basaja a zaman aure (1)

Basaja a zaman aure (1)

Tare da AMINA YUSUF ALI Sannunku da jimirin karatun shafin Zamantakewa na jaridarku mai farin jini ta Manhaja! A wannan mako mun kawo muku yadda wasu ma'aurata suke yin basaja a zaman aure. Wanda abu ne da yake taka muhimmiyar rawa wajen kawo rikici a gidajen aure har ma idan abu ya yi kamari ya kai ga rusa auren gabadaya. To wai meye basaja? Na san mai karatu zai so ya san ma'anar basaja. Basaja kamar sani azancin maganar nan ne da ake cewa kitsen rogo. Wannan azancin na nufin kamar yadda muka sani rogo yana da fari, musamman danyensa…
Read More
Shin a Nijeriya ma ana yin digirin siyarwa?

Shin a Nijeriya ma ana yin digirin siyarwa?

Daga MUSA AYUBA IBRAHIM Akwai wani da ya nuna min wani babban ma'aikacin gwamnati ya ce: su na shekararsu ta karshe suka fara ganin sa, yana shigowa jifa-Jifa lakca ya zo su gaisa, bayan gama jami'ar sai ga sunan sa a jerin waɗanda suka kammala digiri. Ba su san shi ba tun daga farko sai shekarar karshe a zango karshe. Wani dan uwa na an tava masa tallan Irin wannna digirin a wata jami'a a kan wani i adadin kudi amma na bashi shawarar hakura gaskiya duk da har samfuri sun nuna masa da misalan mutanen da aka musu. Saboda…
Read More
Mu mayar da hankali ga yin gwaji kafin aure

Mu mayar da hankali ga yin gwaji kafin aure

Tare da ABBA ABUNAKAR YAKUBU Zainab wata matashiya ce da ke koyon aikin jinya, kuma take daf da daidaita zancen aure tsakaninta da wanda take so ta aura. Sanin muhimmancin yin gwajin kwayoyin halittar jini ga aurenta, ya sa ta garzaya domin duba nau'in kwayar halittar jininta a wani asibiti da ke cikin garin Katsina. Sai dai ga mamakinta sakamakon da ya fito ya tsoratata ganin cewa tana dauke ne da nau'in genotype mai AS, savanin abin da take sa rai ta gani na AA, wanda a cewarta akasari 'yan gidansu ke da shi. Babu shakka wannan sakamako ya girgiza…
Read More