02
Feb
Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Wa’adin da Gwamnan Ondo Rotimi Akeredolu, ya bai wa Fulani makiyaya su fice daga dazukan jihar sa, ya haddasa muhawara mai zafi tsakanin kudanci da arewacin Nijeriya. Muhawarar ta dogara ga yadda mai sharhi ko ra’ayi ya ke ganin abun. Ga masu ɗaukar makiyaya ko Fulani makiyaya cewa ’yan Arewa ne ko ma ’yan’uwan su ko ma a ce su na dangantaka da Musulunci ko da ma a iya samun mabiya adddinin Kirista a cikin su da waɗanda ba su san ko “Ba Sin Mi Ara Ba...” to, za su ɗauki wa’adin da Akeredolu ya ba…
