Daga ABUBAKAR A BOLARI, Gombe
A wani sabon yunƙuri na ciyar da harkokin karatu gaba da bunƙasa ilimi a Jihar Gombe, Gidauniyar Danbayo’s Foundation ta sake kai tallafin kayayyakin karatu ga wasu makarantu a yankin ƙaramar hukumar Billiri, lamarin da ke nuna ci gaba da jajircewarta wajen tallafa wa ɗalibai da malamai.
Wannan shi ne karo na biyu da gidauniyar ke gudanar da irin wannan shiri, wanda ke da manufar sauƙaƙa wa yara samun kayan karatu, inganta aikin malamai da kuma taimakawa ƙoƙarin gwamnati na samar da ingantaccen ilimi ga kowane yaro.
Gidauniyar, wadda Ambasada Yusuf Musa Danbayo ya kafa, ta bayyana cewa tallafin wani ɓangare ne na ƙudurin ta na taimaka wa al’umma, musamman masu ƙaramin ƙarfi da waɗanda ke buƙatar tallafi domin inganta rayuwarsu.
Danbayo, wanda kuma mai taimakawawa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ne a harkokin tsaro da mulki, ya kafa gidauniyar ne domin bayar da agaji ga mutane da iyalan da ke cikin buƙata, tare da gudanar da shirye-shiryen jin ƙai da bunƙasa al’umma.
A wannan karon, tallafin ya shafi makarantu da ke yankunan Billiri ta Gabas da Billiri ta Yamma, ciki har da Tal Central Primary School, inda aka raba kayayyakin karatu domin sauƙaƙa wa ɗalibai da malamai gudanar da ayyukansu na yau da kullum.
Kayayyakin da aka raba sun haɗa da littattafan rubutu guda 500, ma’aunai, alƙaluman biro, fensir, masu aske fensir da goge-goge, kowanne guda 500, tare da rajistar aji, littattafan tsara darasi, alƙaluman rubutu a allo da goge allo domin malamai.
A cewar gidauniyar, samun waɗannan kayayyaki zai taimaka wajen rage nauyin da ke kan iyaye, musamman waɗanda ba su da isasshen ƙarfin tattalin arziki na sayen dukkan kayan karatun da yaransu ke buƙata.
Ta jaddada cewa ilimi na daga cikin muhimman hanyoyin da za a bi wajen samar da makoma mai kyau ga yara, tare da taimaka musu wajen gano basirarsu da samun damar bayar da gudummawa ga ci gaban al’umma.
A yayin ziyarar, Danbayo, wanda ke riƙe da sarautar gargajiya ta Dallatun Doma Gombe, ya kai ziyarar girmamawa ga Mai Tangale, Mai Martaba Malam Danladi Sunusi Maiyamba, domin neman albarka da addu’o’in samun nasara ga shirye-shiryen gidauniyar.
Ziyarar ta kuma ƙara jaddada muhimmiyar rawar da sarakunan gargajiya za su iya takawa wajen bunƙasa ilimi, ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kai, da kuma samar da ci gaba mai ɗorewa a cikin al’umma.
Gidauniyar ta yaba wa shugabannin makarantu, malamai, iyaye, sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma bisa haɗin kai da goyon bayan da suke bayarwa wajen ganin an cimma manufofin shirin.
Ta kuma tabbatar da aniyarta ta ci gaba da tallafa wa yara da sauran masu buƙata, tana mai cewa kowane yaro ya cancanci samun damar ilimi ba tare da la’akari da halin tattalin arzikin iyalinsa ba.
Ƙarƙashin taken “Together We Bring Hope”, wato “Tare Muke Kawo Fata”, Danbayo’s Foundation ta ce za ta ci gaba da ƙoƙarin ƙarfafa tunani, kare rayuka, yi wa bil’adama hidima da kuma sauya rayuwar al’umma zuwa mafi alheri.
