INEC, ’yan sanda da hafsoshin tsaro za su tattauna kan keta yarjejeniyar zaman lafiya sau 109

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya gargaɗi jam’iyyun siyasa da magoya bayansu da kada su mayar da babban zaɓen 2027 fagen daga, inda ya buƙace su da su gudanar da yaƙin neman zaɓe cikin zaman lafiya, su mutunta haƙƙin sauran ’yan siyasa, tare da guje wa duk wani abu da zai iya kawo cikas ga tsarin zaɓe.

Amupitan ya ce ƙaruwar rikicin siyasa, hare-hare kan ’yan jam’iyyu da kuma tsoratar da jama’a na iya kawo illa ga sahihancin zaɓen tun kafin a fara kaɗa ƙuri’a.

Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa wannan gargaɗi ya zo ne a daidai lokacin da ake ƙara nuna damuwa kan rikicin siyasa. Kwamitin Zaman Lafiya na ƙasa ya bayyana kwanan nan cewa jihohi 26 da Babban Birnin Tarayya, Abuja, sun samu rahotannin keta yarjejeniyar zaman lafiya ta ƙasa guda 109 tsakanin 19 ga Agusta zuwa 27 ga Oktoba, 2026. Daga cikin waɗannan, akwai hare-haren siyasa da ayyukan ’yan daba guda 33.

Amupitan ya bayyana hakan ne ranar Talata a Abuja, yayin wani babban taron tsaro da Sufeto-Janar na ’Yan Sanda, Tunji Disu, ya kira tare da shugabannin jam’iyyun siyasa da sauran masu ruwa da tsaki gabanin babban zaɓen 2027.

Shugaban INEC, wanda ya ce hukumar ta dakatar da wani taronta domin halartar tattaunawar, ya bayyana lamarin a matsayin abin damuwa, yana mai nuna fargaba kan hare-hare da ake kai wa ’yan Nijeriya da ’yan jam’iyyun siyasa.

Ya ce: “Idan na ce muku a matsayina na shugaban INEC ba na cikin damuwa kan yanayin rikici da ayyukan ’yan daba, da hare-hare kan ’yan Nijeriya da ’yan jam’iyyun siyasa waɗanda ya kamata mu yi aiki tare da su, to zan yaudari kowa. Lamarin abin damuwa ne.”

Amupitan ya tuna cewa a baya ya buƙaci shugabannin siyasa da kada su mayar da zaɓe fagen daga, maimakon haka su ɗauke shi a matsayin damar da jam’iyyun siyasa za su gabatar wa masu zaɓe da manufofinsu, shirye-shiryensu da ra’ayoyinsu.

Ya ce: “Za ku tuna cewa a jawabin da na yi wa shugabannin jam’iyyun siyasa da mambobin Kwamitin Zaman Lafiya na ƙasa ranar 18 ga Agusta, 2026, na jaddada wani muhimmin batu: kada mu mayar da zaɓe fagen daga. Yayin da muke ci gaba da yaƙin neman zaɓe, ya kamata mu ɗauki zaɓe a matsayin gasa ta neman aiki ta hanyar gabatar da cancanta.”

Ya yi jayayya da cewa ya kamata jam’iyyun siyasa su mayar da hankali wajen neman ƙuri’un ’yan Nijeriya ta hanyar manufofinsu da shirye-shiryensu, maimakon shiga ayyukan da ke barazana ga tsaro da lafiyar jama’a.

A cewarsa, kundin tsarin mulki ya tanadi cewa ikon mulki na hannun al’umma, don haka tsaro da walwalarsu ya kamata su kasance a sahun gaba cikin abubuwan da gwamnati ke ba fifiko.

Shugaban INEC ya gargaɗi cewa rikicin siyasa na iya hana masu zaɓe shiga zaɓe, lamarin da zai kawo illa ga tsarin dimokuraɗiyya da sahihancin zaɓen.

Ya ce: “Idan masu ruwa da tsaki ba za su iya taruwa, gudanar da yaƙin neman zaɓe ko shirya kansu, tare da bayyana ra’ayoyinsu cikin ’yanci ba, to an riga an kawo cikas ga tsarin siyasa tun kafin ranar zaɓe.

“Kuma wannan shi ne manufar irin wannan rikici: tsoratar da jama’a domin kada su fito su kaɗa ƙuri’unsu.”

Saboda haka, Amupitan ya buƙaci ’yan sanda su kama, su gudanar da bincike, sannan su tabbatar an gurfanar da mutanen da ke da hannu a rikicin zaɓe, musamman waɗanda ke da alhakin kalaman yaƙin neman zaɓe masu tayar da hankali da kuma amfani da ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai.

Ya yi nuni da sashe na 95, 96 da 97 na Dokar Zaɓe ta 2026, waɗanda suka tanadi ƙa’idojin gudanar da tarukan siyasa, ayyukan yaƙin neman zaɓe da aka haramta, da kuma barazanar tashin hankali.

Ya ce sashe na 95 na dokar ya wajabta wa kwamishinonin ’yan sanda na jihohi da na Babban Birnin Tarayya samar da isasshen tsaro ga tarukan siyasa da jerin gwano.

Shugaban INEC ya kuma gargaɗi jam’iyyun siyasa da kada su shirya, samar wa ko riƙe ƙungiyoyin tsaro da ƙungiyoyin masu goyon bayan siyasa domin ayyukan yaƙin neman zaɓe, yana mai cewa irin waɗannan ayyuka na iya jefa sauran ’yan siyasa da jama’a cikin barazana.

Ya jaddada cewa wajibi ne ’yan sanda su kare ayyukan siyasa da doka ta amince da su, ba tare da hana su ba. Sai dai ya nanata cewa jam’iyyun siyasa da ’yan takara dole ne su bi ƙa’idojin sanar da hukumomi kafin shirya tarukan siyasa da jerin gwano.

Amupitan ya kuma bayyana cewa INEC za ta kira taron tsaro ranar Alhamis, 26 ga Nuwamba, tare da ’yan sanda, hafsoshin tsaro da sauran mambobin Kwamitin Tuntuɓa na Hukumomi Kan Tsaron Zaɓe, domin tattauna sabbin barazanar tsaro da kammala ƙa’idojin tsaro na babban zaɓen 2027.

Ya kuma yi kira ga jam’iyyun siyasa da su shiga atisayen gwajin tantance masu zaɓe da aika sakamakon zaɓe da INEC za ta gudanar a faɗin ƙasa ranar Asabar, 28 ga Nuwamba.

A cewarsa, atisayen zai gwada ingancin na’urar tantance masu zaɓe ta BɓAS, hanyoyin tantance masu zaɓe da kuma aika sakamakon zaɓe gabanin babban zaɓen.

Wannan gargaɗi ya zo ne a daidai lokacin da ake ƙara nuna damuwa kan rikicin siyasa da keta yarjejeniyar zaman lafiya ta ƙasa gabanin babban zaɓen 2027.

Kwamitin Zaman Lafiya na ƙasa ya bayyana kwanan nan cewa jihohi 26 da Babban Birnin Tarayya sun samu rahotannin keta yarjejeniyar guda 109 tsakanin 19 ga Agusta zuwa 27 ga Oktoba, 2026. Rikicin siyasa da ayyukan ’yan daba sun kai 33 daga cikin abubuwan da aka ruwaito.

By ukarofi