Tinubu ya nemi Majalisa ta rage kasafin kuɗin 2026 daga tiriliyan N68.323 zuwa tiriliyan N65.176

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci Majalisar Dokoki ta ƙasa ta soke tare da sake kafa dokar kasafin kuɗin shekarar 2026, inda ya gabatar da shawarar rage jimillar kuɗin kasafin daga naira tiriliyan 68.323 zuwa naira tiriliyan 65.176, a wani yunƙuri na daidaita tsarin kashe kuɗaɗen gwamnatin tarayya da wajibai da albarkatun da ake da su.

News Point Nigeria ta ruwaito cewa buƙatar Shugaban ƙasar na ƙunshe ne cikin wasiƙar da ya aike wa Majalisar a ranar 20 ga Nuwamba, 2026, wadda Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ya karanta yayin zaman Majalisar na ranar Talata.

A cikin wasiƙar, Tinubu ya bayyana cewa sauye-sauyen da yake son yi na da nufin daidaita kasafin kuɗin shekarar 2026 da muhimman alƙawura da wajibai na kuɗi da gwamnati ke da su, tare da albarkatun da ake da su, domin inganta sahihanci da aiwatar da kasafin ayyukan raya ƙasa.

Shugaban ƙasar ya ce shawarar za ta taimaka wajen daidaita wasu kuɗaɗen da kamfanin NPCL ya kashe a madadin tarayya, biyan gibin kuɗaɗen hidimar bashi, amincewa da takardun izinin kashe kuɗin ayyukan raya ƙasa da ƙarin alƙawuran kuɗi, da kuma samar da kuɗin mayar wa ma’aikatu, hukumomi da sassa daban-daban na gwamnati (MDAs), da kuma asusu na musamman.

Tinubu ya ce: “Wannan zai daidaita wasu kuɗaɗen da NPCL ta kashe a madadin tarayya, magance ƙarancin tanadin kuɗaɗen hidimar bashi, amincewa da takardun izinin kashe kuɗin ayyukan raya ƙasa da ƙarin alƙawuran kuɗi, tare da samar da kuɗin mayar wa ma’aikatu, hukumomi da sassa daban-daban na gwamnati da kuma asusu na musamman.”

Ya bayyana cewa a ƙarƙashin sabon tsarin, yawancin kuɗaɗen ayyukan raya ƙasa da aka ware wa ma’aikatu da hukumomi sun ta’allaka ne kan kuɗaɗen da aka riga aka ba da izinin kashewa, yayin da aka ƙara wasu sabbin kuɗaɗen ayyukan raya ƙasa da na gudanarwa domin aiwatar da muhimman ayyukan ƙasa.

A cewarsa, ƙarin kuɗaɗen sun fi karkata ne ga kammala muhimman ayyukan tituna, kare noman amfanin gona, rage kuɗin samar da kayayyaki, inganta amfanin gona, sauƙaƙa hanyoyin kai kayayyaki kasuwa da kuma magance matsalolin ƙarancin ruwa.

Tinubu ya ce: “A ƙarƙashin sabon tsarin, jimillar kuɗin kashewa ita ce naira tiriliyan 65.176, sabanin naira tiriliyan 68.323 da aka amince da su a kasafin da ake da shi, yayin da ake hasashen samun kuɗaɗen shiga na gwamnatin tarayya, ciki har da na kamfanonin gwamnati, zai kai naira tiriliyan 33.720. Jimillar kuɗaɗen ayyukan raya ƙasa kuma za ta kai naira tiriliyan 26.232.”

Shugaban ƙasar ya ƙara da cewa gibin kasafin kuɗin, ciki har da lamunin da aka ware wa wasu ayyuka na musamman, zai ci gaba da kasancewa naira tiriliyan 31.457, wanda ya kai kashi 5.64 cikin 100 na jimillar tattalin arzikin ƙasa (GDP).

Ya ce sauye-sauyen na da nufin ba da fifiko ga wajibai da aka riga aka ɗauka, ƙarfafa sahihanci da aiwatar da kasafin ayyukan raya ƙasa, tare da kiyaye tsarin kashe kuɗi cikin taka-tsantsan.

Tinubu ya kuma bayyana cewa sabon shirin karɓar bashi zai ci gaba da kasancewa naira tiriliyan 29.218, wanda ya ƙunshi naira tiriliyan 18.428 na bashin cikin gida da naira tiriliyan 10.790 na bashin ƙasashen waje.

Ya ce: “Shirin karɓar sabon bashin ƙasashen waje na dala biliyan 7.7, wanda ya yi daidai da kusan naira tiriliyan 10.368 bisa farashin dala ɗaya kan naira 1,346.50, an tsara shi ne domin biyan kuɗin bashin ƙasashen waje da aka riga aka tanada a kasafin, kuma ba zai ƙara yawan bashin da aka amince a karɓa ba.”

Shugaban ƙasar ya buƙaci Majalisar Dokoki ta ƙasa ta yi gaggawar nazari da amincewa da kudirin, domin ba da damar aiwatar da sabon kasafin cikin tsari tare da biyan wajibai da ake bin gwamnati.

A watan Afrilun 2026, Tinubu ya sanya hannu kan dokar kasafin kuɗin shekarar 2026 mai naira tiriliyan 68.323, bayan da ya fara gabatar da kasafin kuɗin na naira tiriliyan 58.47 ga Majalisar Dokoki ta ƙasa a watan Disamban 2025.

Sai dai a ranar 31 ga Maris, 2026, Shugaban ƙasar ya nemi a ƙara naira tiriliyan 9.81 a kan adadin kasafin da ya gabatar da farko, wanda hakan ya kai jimillar kuɗin kasafin zuwa naira tiriliyan 68.323.

By ukarofi