Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hare-haren sama da rundunar sojin Nijeriya ta kai kan ’yan ta’adda sun yi sanadin kashe mutum 37 tare da lalata motocin ’yan ta’addan guda huɗu, a yayin wasu hare-haren ƙazanta da aka gudanar a sassan Jihar Borno tsakanin ranakun 16 zuwa 23 ga Nuwamba.
Hare-haren, waɗanda rundunar haɗin gwiwa ta musamman ta Arewa maso Gabas, Operation HAɗIN KAI (OPHK), ta gudanar ta amfani da jiragen yaƙi, sun kuma lalata wani wurin da ’yan ta’adda ke amfani da shi wajen taruwa tare da dakile wasu ayyukan da ake zargin suna da alaƙa da shirya bama-bamai na IED.
Muƙaddashin Jami’in Yaɗa Labarai na Hedikwatar Rundunar Haɗin Gwiwa ta Operation HADIN KAI, Kyaftin Mohammed Goni, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Maiduguri.
Goni ya ce an kai hare-haren ne a wurare biyar, bayan samun sahihan bayanan sirri da kuma ci gaba da gudanar da ayyukan leƙen asiri, sa ido da bincike ta sama (ISR).
Ya bayyana cewa a ranar 16 ga Nuwamba, sojoji sun kai wani hari na rigakafi a arewa maso gabashin Monguno, inda suka kashe ’yan ta’adda 10 bayan bayanan sirri sun nuna cewa suna shirin matsowa kusa da wuraren da sojoji suke.
Ya ƙara da cewa a ranar 17 ga Nuwamba, wani hari da aka kai a Arina Chiki ya lalata wurin da ’yan ta’adda ke amfani da shi wajen taruwa.
Haka kuma, hare-haren da aka kai a ranar 20 ga Nuwamba a Kerenoa da Fage sun lalata motocin ’yan ta’adda guda uku, ciki har da motar da ake zargin tana da alaƙa da ayyukan ƙera ko shirya bama-bamai na IED.
A cewarsa, a ranar 23 ga Nuwamba, sojoji sun kai wani hari a yankin Tumbuma Baba, inda suka lalata wata motar ’yan ta’adda.
Muƙaddashin jami’in yaɗa labaran rundunar ya ce a wani ƙarin samame da aka gudanar a yankin, an gano wasu ’yan ta’adda takwas suna taruwa a ƙarƙashin wata bishiya, inda daga bisani aka kashe su ta hanyar wani hari na sama da aka kai da cikakken nufin kai wa inda suke.
Ya ce ayyukan sun raunana ƙarfin ’yan ta’addan, sun kawo cikas ga zirga-zirgarsu da hanyoyin samar musu da kayayyakin aiki, tare da jaddada aniyar rundunar na ci gaba da kai hare-hare tare da haɗin gwiwar dakarun ƙasa.
Goni ya kuma buƙaci al’umma su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai cikin gaggawa domin taimaka wa ayyukan sojojin da ake gudanarwa.
