Makarantar SAS ta cika shekara 90 tana fitar da muhimman mutane

Spread the love

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano

Makarantar koyar da harshen Larabci da ke Kano (SAS) ta yi bikin murnar cika shekara 90 da kafuwarta, tana mai fitar da fitattun mutane da suka yi fice a fannoni daban-daban a duniya.

Da yake zantawa da manema labarai, Shugaban ƙungiyar ɗaliban Makarantar, reshen Jihar Kano, Malam Muhammad Lawan Abdu, ya ce makasudin shirya taron a wannan lokaci shi ne domin su taya junansu murna bayan kammala karatu a makarantar.

Ya ce makarantar tana yaye manyan mutane tun daga kafuwarta zuwa yanzu, waɗanda ba a Nijeriya kaɗai ba, har ma a duniya ake alfahari da su.

Ya bayyana cewa nasarorin da makarantar ke samu sun samo asali ne daga kasancewarta mai ɓangarori biyu, waɗanda suka haɗa da na boko da na Islamiyya. Hakan ya sa ɗalibai ke samun ilimi iri biyu a lokaci guda.

A nasa ɓangaren, Daraktan makarantar ta SAS, Malam Abubakar Idris Gwammaja, ya ce an shirya taron na tsawon kwanaki biyu. A rana ta farko za a yi karatun Alƙur’ani da addu’o’i ga waɗanda suka kafa makarantar, irin su Sarkin Kano Alhaji Abdullahi Bayero, Wazirin Kano Gidado, Walin Kano Malam Suleiman da sauran shugabannin makarantar.

Ya ce za a yi addu’o’in ne ga dukkan shugabannin makarantar tun daga na farko, Sheikh Bashir Alrayya, har zuwa na yanzu, da waɗanda suka rasu, da tsofaffin ɗalibai, da kuma makarantar kanta, domin neman ƙarin ci gaba da ɗaukaka.

Ya bayyana cewa ƙungiyoyin ɗaliban makarantar suna bayar da muhimmiyar gudunmawa wajen ci gabanta ta hanyar samar da kayan karatu, gyaran ajujuwa, bandakuna da wuraren zama ga ɗalibai.

Ya ƙara da cewa makarantar na samun ci gaba ne sakamakon addu’o’in waliyyan da suka kafa ta, waɗanda suka ci gaba da yi mata addu’a tun daga lokacin kafuwarta har zuwa yanzu. Hakan ya taimaka mata wajen bunƙasa da yaye manyan mutane a ƙasar nan waɗanda ke bayar da gudunmawa ga ci gaban al’umma.

Shugaban ya kuma yaba wa waɗanda suka shirya taron, yana mai cewa sun yi abin a yaba wajen shirya wannan gagarumin biki da ba a taɓa yin irinsa a baya ba.

ɗaya daga cikin tsofaffin ɗaliban makarantar, wanda ya kammala karatu a shekarar 1975 kuma farfesa ne a tsangayar koyar da aikin jarida a Jami’ar Bayero da ke Kano, Farfesa Gausu Ahmad, ya ce suna cikin murnar sake haɗuwa da juna bayan shekaru masu yawa da suka kammala makarantar.

Ya bayyana makarantar a matsayin uwa a gare su, domin ita ce ta yaye su har suka zama wasu a cikin al’umma. Ya ƙara da cewa ana gudanar da ayyuka da dama na ci gaban al’umma a makarantar, kamar bitar aikin Hajji, ɗaukar jarabawa, tarurruka da sauran al’amuran yau da kullum.

Taron ya samu halartar tsofaffin ɗaliban da suka kammala makarantar shekaru da dama da suka wuce, tsofaffin shugabannin makarantar da sauran al’umma domin taya murnar wannan rana.

By ukarofi

Leave a Reply