Jam’iyyar ADC ta yi garambawul na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓenta a Zamfara

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau 

Dan takarar gwamnan jihar Zamfara a ƙarƙashin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Hon. Bilyaminu Yusuf Shinkafi, ya bayyana cewar Jam’iyyar ta kaddamar da wasu sauye-sauye a kwamitin yaƙin neman zaɓensa.

Hakazalika ya bayyana cewar cikin saute sauyen da aka gudanar sun kunshi cire wasu mambobi daga cikin kwamitin bayan samun korafe-korafe da ra’ayoyin masu ruwa da tsaki.

Shinkafi ya bayyana hakan ne cikin ƙarin bayani kan jerin sunayen kwamitin yaƙin neman zaɓensa na farko, wanda aka rabawa manema labarai a Gusau ranar Litinin.

Ya ce sauye-sauyen sun biyo bayan shawarwari da tattaunawa da masu ruwa da tsaki, inda aka cire wasu daga cikin mambobin kwamitin sakamakon korafe-korafe da aka gabatar ta hanyoyin sadarwa na jama’a da kuma na sirri.

Haka kuma, ɗan takarar ya fayyace tsarin shugabancin tafiyar yaƙin neman zaɓen, inda ya bayyana cewa an tsara mukamai daban-daban domin tabbatar da ingantaccen haɗin kai tsakanin jam’iyya, ’yan takara da kwamitin yaƙin neman zaɓe.

Shinkafi ya ce shi ne zai jagoranci harkokin dabarun yaƙin neman zaɓe gaba ɗaya, tare da haɗa kan dukkan ’yan takarar ADC a jihar.

Ya bayyana Malam Shehu Maishanu Gulubba a matsayin wanda zai jagoranci tsarin gudanarwar jam’iyyar a matakin jiha, yayin da Hon. Shehu Mohammed Gusau aka naɗa Darakta-Janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen gwamna, wanda zai jagoranci gudanar da ayyukan kamfen ɗin.

Wannan mataki na zuwa ne yayin da ɗan takarar ke ƙoƙarin ƙarfafa tsarin jam’iyyar tare da daidaita ayyukanta domin tunkarar zaɓen gwamna mai zuwa.

Shinkafi ya ce ADC na da ƙudirin gina tafiyar siyasa mai tafiya da kowa, ingantaccen tsari da kuma mayar da hankali kan sakamako, domin samun nasara a zaɓe da kuma dawo da ci gaba, wadata da martabar al’ummar Zamfara.

“Mun ƙuduri aniyar gina tafiyar siyasa mai haɗa kowa, mai ingantaccen tsari da kuma mayar da hankali kan sakamako, wadda za ta iya kai ADC ga nasara tare da dawo da wadata da martabar jihar Zamfara.”

“Tare, za mu dawo da martabar Zamfara, mu tabbatar jihar ta kasance cikin aminci don samun nasarar mu a zaben dake tafe”

By ukarofi

Leave a Reply