Daga MUHAMMAD SADISU ABUBAKAR a Birnin Kebbi.
Daraktan ayyuka na gidan gwamnati da ke Birnin Kebbi, Alhaji Bashiru Abubakar Member, ya rarraba ma ƙungiyoyin manoma buhuhunan takin-zamani, sannan kuma ya bai wa ƙananan ‘yan kasuwa guda sittin, Naira 10,000 kowanensu da nufin haɓɓaka masu jari.
A lokacin taron da aka yi ranar Alhamis a Unguwar Maƙerar-Gandu da ke Birnin Kebbi, Bashiru Member ya ce wannan karamcin da ya yi, biyayya ne ga umurnin Gwamna Nasir Idris, cewar duk manyan muƙarraban gwamnati da masu riƙe da matsayin siyasa, su riƙa taimakawa al’ummarsu ko kuma ya sauke su daga muƙamansu.
Manyan mutanen da suka halarci taron sun bada gudunmawar naira dubu ɗari biyar da nufin a ƙara yawan masu cin moriyar shirin.
Shi kuma shugaban jam’iyyar APC na mazabar Nasarawa ta biyu, Babangida Mai-Gwandu, ya yi kira ga dukkan magoya bayan jam’iyyar APC su jefa ƙuri’arsu tururu ga jam’iyyar APC sama da ƙasa, su guji yin gamin-gambiza.
Ya ce su jefa kuri’arsu ma shugaban ƙasa Tinubu da wakilan majalisar dattijai da ‘yan Majalisar wakilai ta tarayya da Gwamna Nasir Idris na Kebbi da kuma ‘yan majalisar jihar a ƙarƙashin jam’iyyar APC a zaɓuɓbuka masu zuwa.
Mai-Gwandu ya ce su guji jefa kuri’a ta wake da shinkafa, amma su jefa ma APC sak daga sama har ƙasa.
