FIFA ta tabbatar da kutse a shafin yanar gizonta bayan sojan gonan jami’anta

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Alhamis, 26 ga Nuwamba, 2026, Hukumar Kula da Harkokin Ƙwallon Ƙafa ta Ƙasa-da-ƙasa FIFA, ta tabbatar da cewa an samu kutse a shafinta na yanar gizo, wanda ya yi sanadiyyar samun wasu bayananta daga ɓangaren masu farmakin. A cewar rahotanni, wata ƙungiyar ‘yan yahoo da ake kira Hansome Boy Hacking Club ta yi iƙirarin hannu a aukuwar lamarin inda ta ce ta yi haka ne ta hanyar amfani da sunan jami’anta da nufin samun wasu kuɗaɗe.

Ƙungiyar ta kuma yi iƙirarin samun bayanai masu nauyin jimillar gigabytes 12, ciki har da takardun shaida da rahotannin kuɗaɗe kuma ta fara wallafa hotunansu da ta ɗauka a kafafen yanar gizo a makon da ya gabata.

Duk da iƙirarin ‘yan kutsen, majiyoyi masu kusanci da al’amarin sun nuna cewa bayanan da suka samu na wakiltar kaso 0.1 ne kaɗai na baki ɗaya bayanan da hukumar take da su a kwamfuta. Rahotanni da dama sun ce, wannan hari an nufi aiwatar da shi ne akan FIFA kai-tsaye a madadin wasu ɗaiɗaikun mutane.

A wata sanarwa, wani kakakin FIFA ya yi tir da aukuwar al’amarin samun bayanan hukumar ba bisa doka ba, yana mai bayyana hakan a matsayin muhimmin al’amari da ba za a lamunta ba ganin yadda hakan yake matsayin tauye ‘yancin ɓoye sirri ga hukumar. FIFA ta ce tana aiki da hukumomin da suka dace wajen warware matsalar duk da cewa ba ta bayyana ainihin ranar da al’amarin ya faru ba, mutane ko ƙungiyoyin da hakan ya shafa.

By Babaji

Leave a Reply