Daga SULEIMAN HUSSAINI D /KUDU a KANO
Shugabar matan jam’iyar ADC reshen jihar Kano Hajiya Murja Aliyu ta bayyana burin da suke da shi akan ɗan takarar su na shugabancin ƙasa Alhaji Atiku Abubakar shine ya karɓi ragamar shugabancin ƙasar nan a zaɓen shekara mai zuwa.
Hajiya Murja ta sanar da hakan ne a saƙon ta na taya murnar cika shekara 80 da ɗan takarar jam’iyar ta su ya yi ranar Laraba a ofishin ta da ke Kano. Inda tace suna taya shi murnar wannan rana da Allah ya nuna masa wanda a cewar ta tsawon wannan shekaru da ya yi, ya yi sune cikin hidimtawa al’umma.
Ta kuma ƙara da cewa Atiku ya bada gudunmawa wajen cigaban siyasar ƙasar nan dama al’ummar cikin ta duba da yadda a kullum yake fafutukar ganin cewa talaka ya samu yanci a ƙasar nan.
Kazalika, shugabar matar tace babban burin da suka sanya a gaba shine na ganin ɗan takarar na su ya kai ga nasarar cinye zaben da za’a gudanar a shekara mai zuwa. Inda tace suna da yaƙinin cewa da zarar sun sami nasarar zaɓen, ba shakka zai gyara duk wasu abubuwa da aka ɓata su a baya.
Ta kuma yi kira ga al’ummar ƙasar su tabbata sun zaɓi Atiku Abubakar domin shine kaɗai jirgin ceton al’umma. ” mun san idan ya sami ƙasar, an sami gyara, zai gyara ƙasar nan duk abin da ya lalace zai gyara shi da yardar Allah”.
