Daga AISHA ASAS
ƙasar Ghana ta fara halartar bikin baje kolin littattafai na ƙasa da ƙasa na Sharjah (Sharjah International Book Fair) a karon farko, inda ta yi amfani da damar wajen gabatar da marubutanta, littattafai da kuma wasu daga cikin al’adun gargajiyarta ga masu karatu daga sassa daban-daban na duniya.
Wannan halarta ta ƙasar ta zo ne a bugu na 45 na bikin, wanda aka gudanar a birnin Sharjah na ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa.
A cikin littattafan da aka gabatar akwai na yara, ƙagaggun labarai da kuma waɗanda suka samo asali daga tatsuniyoyi da al’adun gargajiyar Ghana.
Daga cikin marubutan da suka wakilci ƙasar akwai Oswald Okaitei, wanda ya gabatar da littafinsa mai suna ‘First Harvest’, da Ruby Yayra Goka, marubuciyar ‘Mama’s Amazing Cover Cloth’.
Haka kuma, marubuciyar littattafan yara da matasa, Elizabeth-Irene Baitie, ta halarci bikin tare da littafinta ‘Flying Up the Mountain’.
Wani abin lura shi ne yadda Ghana ta yi amfani da kayan gargajiyarta wajen ƙawata rumfar da ta tanada a wurin baje kolin, inda aka yi amfani da zanen Kente, wanda ke daga cikin fitattun kayan gargajiyar ƙasar.
Kokui Selormey daga ofishin jakadancin Ghana da ke Dubai ta bayyana cewa sun fara tunanin halartar bikin ne bayan da suka ziyarce shi a shekarar da ta gabata, inda suka lura cewa babu wakilcin marubuta da masu wallafa littattafai daga ƙasarsu.
Ta ce sun ga dacewar kawo marubutansu da labaransu domin masu karatu daga sauran ƙasashe su samu damar sanin adabi da al’adun Ghana.
Wannan mataki na da muhimmanci ga marubutan Ghana, domin kuwa halartar irin waɗannan bukukuwa na ba su damar kai ayyukansu ga sababbin masu karatu, tare da samar musu da damar samun karɓuwa a kasuwannin littattafai na duniya.
